Da duminsa: T. B Joshua ya rasu, yana da shekaru 57 a duniya

Da duminsa: T. B Joshua ya rasu, yana da shekaru 57 a duniya

- Fitacce kuma gagarumin Faston nan, TB Joshua ya rasu a ranar Asabar a shekaru 57

- An fara yada labarin mutuwarsa a safiyar Lahadi amma cocinsa ta tabbatar da hakan

- Duk da ba a bayyana hakikanin abinda ya kashesa ba, ya rasu ne bayyana kammala wani shiri

Gagarumar majami'ar dukkan kasashe ta tabbatar da mutuwar Fasto Temitope Balogun Joshua, wanda ya kirkirota.

Fitaccen faston da aka fi sani da T. B Joshua ya rasu ne yana da shekaru 57 a duniya, Daily Trust ta tabbatar.

Rahotanni kan mutuwar Joshua sun fara yawo ne a sa'o'in farko na ranar Lahadi amma kuma ba a tabbatar ba.

KU KARANTA: Gagararriyar kungiyar fashi da makami ta mutum 3 ta shiga hannun 'yan sanda a Ribas

Da duminsa: T. B Joshua ya rasu, yana da shekaru 57 a duniya
Da duminsa: T. B Joshua ya rasu, yana da shekaru 57 a duniya
Asali: Original

Amma kuma a wata takarda da majami'ar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce ya rasu ne bayan yin wani shiri a ranar Asabar.

"Tabbas Ubangiji mai karfin mulki baya yin komai ba tare da ya bayyana shirinsa ga bayinsa ba." - Amos, Surah ta 3, aya ta 7.

“A ranar Asabar, 5 ga watan Yunin 2021, TB Joshua yayi jawabi a gidan talabijin na Emmanuel: "Lokacin komai yana zuwa - lokacin zuwa addu'a da komawa gida yayi bayan bauta."

"Ubangiji ya karba bawansa TB Joshua domin ya huta a gida, kamar yadda ya dace da izinin Ubangiji. Ya sadaukar da lokutansa a duniya wurin bautar Ubangiji. Abinda aka haifesa domin shi kenan, ya rasu yana yi kuma ya mutu a kan shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai farmaki Kano, sun yi luguden wuta tare da sace attajiri

"Kamar yadda TB Joshua yace, "Babbar hanyar amfana da rayuwar nan shine yin abinda ka san ko babu ranka yana nan."

"TB Joshua ya bautawa Ubangiji kuma ya sadaukar da rayuwarsa saboda na baya."

Majami'ar bata sanar da abinda ya kawo mutuwar babban faston ba.

A wani labari na daban, facebook, wata kafar sada zumuntar zamani ta cire tsokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafinsa.

Shugaban kasan a ranar Talata yayi barazanar maganin masu kai farmaki ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta kamar yadda sojoji suka yi wa 'yan tawaye a yakin basasa.

Buhari, soja mai mukamin janar amma wanda yayi ritaya ya yi yakin basasa wanda ya lamushe rayukan sama da mutum miliyan daya, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel