Betta Edu: Jerin Masu Mukamin Da Tinubu Ya Nada Kuma Ya Dakatar/Cire Su Kasa Da Shekara 1

Betta Edu: Jerin Masu Mukamin Da Tinubu Ya Nada Kuma Ya Dakatar/Cire Su Kasa Da Shekara 1

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, biyo bayan zargin karkatar da kuɗi, wanda hakan ya sanya ta zama ta uku da wannan gwamnatin ta cire ko kuma ta dakatar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kakakin Tinubu, Ajuri Ngelale, ya sanar da dakatar da Edu a wata sanarwa a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, inda ya ƙara da cewa nan take an umurci EFCC ta gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake mata.

Masu mukamin da Tinubu ya dakatar
Shugaba Tinubu ya dakatar da wasu masu mukamin da ya nada Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Betta Edu, Concerned Nigerian
Asali: Twitter

Dalilin da yasa Tinubu ya dakatar da Betta Edu

An yi zargin cewa ministar mai shekara 37 tana da hannu a wata badaƙalar kuɗi ta N585,198,500.00, waɗanda aka fitar zuwa cikin wani asusu.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Edu wacce ita ce minista mafi ƙarancin shekaru a majalisar ministocin Tinubu, ta sanya hannu kan wata takarda da ta umurci Akanta Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein, da ta tura kuɗin ga wata Oniyelu Bridget a matsayin tallafi ga marasa galihu a jihohi huɗu.

Sai dai, Edu ba ita ce ta farko ba cikin waɗanda Shugaba Tinubu ya naɗa sannan ya cire su ko ya dakatar da su a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Ga sauran waɗanda Shugaba Tinubu ya naɗa kuma ya dakatar ko ya cire:

Engr. Imam Kashim Imam

Kashim Imam, wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a ranar Juma’a, 13 ga watan Oktoba a matsayin shugaban hukumar FERMA, yana daya daga cikin waɗanda fadar shugaban ƙasa ta sanar da cire shi a ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba.

Imam ɗan shekara 24 a duniya wanda sabon kammala karatu ne ya samu matakin ajin farko, bayan ya kammala karatun Injiniya a jami'ar Brighton da ke ƙasar Ingila.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Hukumar EFCC ta dauki muhimmin mataki bayan Tinubu ya dakatar da ministar jin kai

Naɗin na Imam wanda ɗa ne wajen jigo a jam'iyyar PDP a jihar Borno ya sha suka daga wasu da dama waɗanda suke ganin shekarunsa sun yi kaɗan kuma ba ya da ƙwarewa a irin wannan babban muƙami domin ya kammala NYSC a shekarar 2022.

Halima Shehu

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar hukumar kula da jindaɗin jama'a ta ƙasa (NSIPA) sakamakon zargin karkatar da kuɗi.

An dakatar da ita ne watanni uku bayan majalisar dattawa ta tabbatar da ita a matsayin shugabar NSIPA.

Tinubu Ya Umurci a Binciki Ofishin Betta Edu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin bincike kan ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.

Shugaban ƙasar ya bayar umurnin ne kan zargin karkatar da N37bn daga ma'aikatar a ƙarƙashin jagorancin Betta Edu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng