Akwai Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Sauka, Dangote Ya Sanya Ranar Fara Tace Mai a Matatarsa

Akwai Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Sauka, Dangote Ya Sanya Ranar Fara Tace Mai a Matatarsa

  • Matatar man Dangote ta ce tana sa ran karbar gangar danyen mai miliyan daya na karshe daga kamfanin NNPC a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2023
  • Matatar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda tace tuni ta samu dimbin danyen mai karo na biyar a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, 2024
  • Kawo kayan na karshe dai dai shi ne na shida da kamfanin na NNPC ya yi alkawarin taimakawa matatar man don fara aikin tace mai a wannan watan

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Legas, Najeriya - Matatar Dangote mai karfin bpd 650,000 da ke Legas za ta samu zubin karshe na gangar danyen mai miliyan daya a ranar Litinin 8 ga watan Janairu, 2024, don fara aiki gadan-gadan a matatar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya umarci a yi bincike kan kudin tallafin talakawa N37bn da aka sace a ofishin Betta Edu

Matatar ta karbi laya sau biyar na gangar danyen mai miliyan daya a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2024 daga kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), kamar yadda majiyar Legit ta ruwaito.

An sanya ranar fara tace mai a matatar Dangote
Za a fara tace mai a matatar Dangote | Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Matatar man Dangote ta karbi kaya kashi na 5

Kamfanin ya sanar da shogowar danyen mai kaso na biyar a ranar Juma’a, 5 ga Janairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ci gaban wani muhimmin mataki ne ga kamfanin yayin da yake shirin fara aiki gadan-gadan don taimakawa Najeriya wajen samun dogaro da kai a fannin tace man fetur.

Sanarwa daga kamfanin ta ce, wannan ne karo na biyar da kamfani ya samu kayan daga NNPCL, kuma yana sa ran samun kari nan kusa.

Wani rahoton BusinessDay ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai kamfanin na da ganga miliyan hudu a kasa daga gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dangote ya farfado, ya ci ribar da ba a yi tsammani ba a cikin kasa da mako 1 na 2024

Yaushe za a fara tace mai a Najeriya?

A tun farko, kamfanin ya sanar da fara tace mai a kasar nan a cikin watan Janairun da ake ciki, inda ya bayyana kadan daga abin da yake bukata.

Masana harkar makamashi sun yi has ashen cewa, matatar za ta taka rawar gani wajen tabbatar da an samu wadataccen man fetur da sauran dangoginsa a Najeriya da ma nahiyar Afrika baki daya.

Ya zuwa yanzu, ‘yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda farashin man fetur ke tashi da kuma yadda ya shafi farashin kayayyaki a kasuwanni.

Matar Dangote ba za ta rage farashin mai ba

Sai dai, wani hanzari ba gudu ba, ko zuwa lokacin da matatar kamfanin Dangote da sauran matatun danyen mai za su soma aiki a Najeriya, farashin man fetur ba zai sauka ba.

Wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari ne a lokacin da ya yi hira da gidan talabijin Arise TV a yammacin Alhamis.

Malam Mele Kolo Kyari ya fito karara yake cewa batun a ce farashin litar mai zai sauka da zarar an fara samun fetur a kasar nan sam ba gaskiya ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.