Masu Hawa Intanet da Kira Za Su Shiga Tasku a Najeriya, MTN, Glo, Airtel Za Su Kara Kudin Data
- Kamfanonin sadarwa na neman gwamnatin Tinubu ta amince da bukatarsu ta kara kudin data da katin kiran waya
- Akwai alamun cewa farashin data zai ninku sau 10 zuwa 15% idan gwamnati ta amince da bukatar wadannan kamfanoni
- Wata majiya ta ce har yanzu gwamnati ba ta amince da bukatar ba har sai an fara aiki da kasafin kudin shekarar 2024
Najeriya - Kamfanonin sadarwa na neman gwamnatin tarayya ta ba da damar karin kudin katin waya da data na hawa intanet a kasar nan.
Majiyoyi daga NCC da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani sun shaida wa Daily Trust cewa, masu amfani da layukan waya a Najeriya za su biya Karin 10% zuwa 15% fiye da kudin da suke siyan data a yanzu idan bukatar kamfanonin ta tabbata.
Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kamfanonin sadarwa suka roki gwamnati da ta amince da bukatarsu ta sake yin bitar farashin kudaden kira da data.
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanonin sadarwa ba su kara farashinsu ba tsawon shekaru duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake samu a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zaftare data a hankali
A halin yanzu, wasu sun lura cewa kila kamfanonin sun kasance suna rage karfi da juriyar data don rufe wannan gibi na rashin Karin farashi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar masu lasisin sadarwa ta Najeriya (ALTON) ta bayyana a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023, cewa tsarin kudin kira da data a yanzu ba zai kaisu ga madakata ba.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta biya bukatarsu ba har sai an fara aiki da kasafin kudin shekarar 2024 gadan-gadan, kamar yadda wata majiya ta shaida wa The Cable ta ruwaito.
A cewar majiyar, ana ci gaba da nazari da tattaunawa kan yadda karin ba zai shafi talakawan Najeriya ba.
Kudin da Tinubu zai kashe a data a 2024
A wani labarin, fadar shugaban kasa ta shirya kashe N14.8bn domin sayen data na hawa shafukan yanar gizo, takardu da sauran kudaden da suka shafi katin waya da na'ura mai kwakwalwa a kasafin kudin 2023 da Buhari ya gabatar.
A cikin kasafin kudin, an ce data kadai za a ci na N67.1m a Villa, yayin da takardu da sauran abubuwan da na'ura mai kwakwalwa za ta ci zai kai N79m.
Fashin bakin kasafin kudin ya kuma nuna cewa, za a kashe N35.9m don biyan kudin wutar lantarki yayin da cajin katin tangaraho da ruwan famfo zai ci N306.2m, N6m da N40.6m bi da bi.
Asali: Legit.ng