EFCC Ta Taso Emefiele Gaba, Dangote Ya Wanke Kan Shi Daga Zargin Harkar Daloli

EFCC Ta Taso Emefiele Gaba, Dangote Ya Wanke Kan Shi Daga Zargin Harkar Daloli

  • EFCC tana bincike na musamman a kan zargin karkatar da Daloli da kamfanoni su ka yi a shekarun baya
  • Kamfanoni fiye 80 ake tuhuma cewa an ba su kudin kasashen waje ba tare da bin ka’idojin bankin CBN ba
  • Watakila a dalilin haka Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya za tayi shari’a da Godwin Emefiele

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta rubuta takarda zuwa ga kamfanoni fiye da 85 a kan binciken badakalar dala.

Ana zargin bankin CBN ya sabawa ka’idoji wajen rabon kudin kasar waje a lokacin Godwin Emefiele, Punch ta fitar da wannan rahoto.

Shugaban hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta shiga kamfanin Dangote Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

EFCC: Sabon aiki a gaban Godwin Emefiele?

Ana fahimtar akwai yiwuwar a tuhumi Godwin Emefiele da sabon laifin badakalar kudin kasashen waje a shari’ar da ake yi da shi.

Kara karanta wannan

Dangote ya kara shiga matsala bayan hukumar EFCC ta ba shi sabon umarni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta kuma bukaci manyan ma’aikatan kamfanonin da ake bincike su bada rahoton kudin waje da aka ba su cikin shekaru tara.

Wani kamfanoni EFCC ta ke bincike?

Wata majiya a EFCC ta ce an bankado wannan badakala ne bayan binciken Jim Obazee.

Jaridar ta ce ba a iya tabbatar da kamfanonin da ake zargi ba, amma daga ciki akwai kamfanonin Dangote Group da kuma BUA Plc top.

Ma’aikatan kamfanin Dangote Group sun tabbatar da jami’an EFCC sun dura ofishinsu, kuma suna ba su cikakken hadin-kan aiki.

Ma’aikatan kamfanin Dangote sun shaida cewa shirya gabatar da takardun da ake bukata domin EFCC ta ji dadin binciken da ta ke yi.

Rahoton ya ce kamfanin ya nuna babu laifin da aka jefi su da shi na karkatar da Daloli, su ka ce a bankunan waje su ke samun kudi.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Jami'an EFCC sun dura ofishin BUA bayan lalube kamfanin Dangote

Amma kamfanin BUA ya musanya zargin cewa EFCC ta binciki ofishinsa da ke garin Legas.

Badakalar Dala da Emefiele a kamfanoni

A cewar wani ma’aikaci na hukumar EFCC, tsohon gwamnan CBN ya azurta abokansa da daloli lokacin yana ofis ba tare da bin doka ba.

Ana zargin Muhammadu Buhari bai amince da kudin da aka rabawa wasu kamfanonin ba, sakamakon binciken zai fito da lamarin fili.

Idan zancen ya tabbata, lauyoyin EFCC za su shigar da wani sabon karar Mista Emefiele a kotu kwanaki kadan da alkali ya bada belinsa.

Mako guda bayan Abdussamad Rabiu ya hadu da Bola Tinubu, aka kawo rahoto cewa jami'an EFCC sun shiga kamfaninsa da ke garin Legas.

Da alama Hukumar ta na binciken kamfanin BUA PLC kamar yadda aka shiga Dangote Plc.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng