Daga Karshe Iyayen 'Yar Shekara 4 Da Aka Aurawa Dan Shekara 54 Sun Magantu
- Iyayen wata yarinya yar shekaru hudu da aka daura aurensu da tsoho dan shekaru 54 sun yi bayanin cewa wannan al'ada ce don ceto rayuwar yarinyar
- An yi hasashen cewa daurin auren da aka yi a garin Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa ya kasance aure na ceto rai
- Wannan bikin an yi shi ne da niyar yanke alakar da ke tsakanin mutane biyu da ake zaton sun yi aure a rayuwarsu ta baya
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Iyayen yar shekaru hudu da ta auri tsoho dan shekaru 54 sun alakanta abun da suka yi da tsari al'ada domin kare rayuwar yarinyar.
An bayyana auren, wanda ya gudana a garin Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa, a matsayin biki na ruhi da nufin yanke alakar auren da aka kulla a rayuwarsu ta baya.
Da suka fuskanci tawagar GRIT na gwamnatin jihar, wanda suka hada da Dr Dise Ogbise-Goddy da Kizito Andah, iyaye da sauran mahalarta taron sun yi cikakken bayani game da rawar da suka taka a auren da ake zargin an yi wa karamar yarinyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bayyana cewa lamarin, wanda ake kira da "Koripamo," wata al'ada ce a cikin al'ummar Akeddei da nufin kare rayuwar yarinya mai yawan rashin lafiya.
Mutanen sun fayyace cewa bikin ba aure ne a hukumance ba face al'ada inda wani mutum zai biya kudi.
Sun kara da cewar ba dole bane sai mutumin da ya biya kudin ya auri yarinyar, kuma al'ada ba za ta hana yarinyar auren duk wanda take muradi ba a gaba.
Wakilan garin sun jaddada cewar ana iya yi wa kowa "Koripamo" imma maza ko mata a al'adar Ijaw.
Mahaifin amaryar ya magantu
Mista Morris Aboma, mahaifin yarinyar, ya bayyana a yaren Ijaw, cewa yawan rashin lafiyar da yarinyar ke yi ya kai ta ga matakin mutuwa.
Bisa ga al'adar Akeddei, dole ne sai wani mutum ya fanshi ran yarinyar domin ta rayu. Ya jaddada cewar wannan abu baya da alaka da ainahin aure na gaskiya.
Mista Akpos Napoleon, mutumin da abun ya shafa, ya nuna danasani dangane da hayaniyar da mutane suka yi, inda ya kara cewar abun da ya aikata don ceto rayuwar yarinyar ne kawai.
Ya kara da cewar wannan daddiyar al'ada ce wacce ba a yin wasu bukukuwan a zo a gani.
Nigerian Tribune ta nakalto Napoleon yana cewa:
"Amma tun da ta ce idan ban yi abun da ta ce na yi ba za ta mutu, dole na nemi kudi na yi saboda abu ne da ya shafi rayuwa, na gaji da duk wadannan abubuwan."
Cif Moneyman Binabo, basaraken, ya yi karin haske cewa abun da ya faru a Akedde ba aure bane a hukumance kawai al'ada ce.
Ya nuna mamaki ga bukatar yarinyar na yin gagarumin biki tare da cewar mutumin da ya fashin ran nata ba zai yi rayuwa da ita a matsayin miji ba.
Tawagar GRIT sun tabbatar da cewar taron ba aure bane a hukumance kawai al'ada ce.
Sun bayar da tabbacin cewa ba'a yi tarayyar kwanciya da yarinyar ba, kuma wani likitan GRIT ya tabbatar hakan, yana mai cewa babu abun da ya shiga tsakaninta da tsohon.
Gwamnatin Bayelsa ta magantu kan auren yarinya
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin jihar Bayelsa ta sanya baki a haramtaccen auren da aka yi wa wata yarinya yar shekara hudu da wani dattijo dan shekara 54 a garin Akeddei, karamar hukumar Sagbama ta jihar.
Gwamnatin Gwamna Douye Diri ta gayyaci iyayen karamar yarinyar da kuma mutumin mai shekara 54 bayan auren ya yadu a shafukan soshiyal midiya, rahoton Premium Times.
Asali: Legit.ng