Gwamna Zulum Ya Yi Wani Muhimmin Abu Domin Farfado da Bangaren Lafiya a Borno

Gwamna Zulum Ya Yi Wani Muhimmin Abu Domin Farfado da Bangaren Lafiya a Borno

  • Gwamnatin jihar Borno ta amince da biyan kuɗin karatun ɗaliban likitanci mutum 153 ƴan asalin jihar
  • Gwamnatin a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum, ta amince da sakin sama da Naira miliyan 153 domin biyan kuɗaɗen rajistar ɗaliban
  • Ɗaliban da aka fitar da kuɗaɗen domin biya musu kuɗin rajistar na yin karatu ne a jami'ar lafiya da kimiyya ta tarayya dake Azare a jihar Bauchi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta amince da sakin sama da Naira miliyan 55 cikin gaggawa domin biyan kuɗin rajistar ɗaliban likitanci 153.

Gwamnatin a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum, ta amince da hakan ne a wani yunƙuri na farfaɗo da ɓangaren lafiya wanda yake fama koma baya saboda matsalar ƴan tada ƙayar baya, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rusau: Yan kasuwan Kano sun shigar da korafi wurin yan sanda kan Gwamna Abba da Kwankwaso

Gwamna Zulum ya biya kudin karatun dalibai
Gwamna Zulum ya amince da biyan kudin dalibai 153 a Borno Hoto: Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Malam Bala Isa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa, biyan kuɗin ya shafi kuɗin rajistar ƴan asalin jihar Borno mutum 153 da suka shiga jami’ar lafiya da kimiya ta tarayya dake Azare a jihar Bauchi.

Ya ce an kai ɗaliban ne domin yin karatun likitanci, Radiography, Audiology, Epidemiology da statistics, physiotherapy, IT, bayanan lafiya, da dai sauransu.

An yaba da ƙoƙarin Gwamnan

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗan jihar Borno mai suna Malam Muhammad, wanda ya yaba da namijin ƙoƙarin da gwamnan ya yi.

Malam Muhammad ya bayyana cewa biyan kuɗaɗen zai taimaka wajen bunƙasa kiwon lafiya a jihar, domin idan suka kammala karatunsu jihar za ta amfana da abin da suka karanta.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke Halima Shehu shugabar hukumar NSIPA bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da ita

Ya yi kiran da a sanya wani tsari wanda zai sanya idan ɗaliban sun kammala karatunsu, za su dawo jihar ta ci gajiyar abin da suka karanta na aƙalla shekara biyar.

Gwamna Zulum Ya Samar da Motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya samar da motoci 300 domin jigilar manoma a jihar Borno.

Gwamnan ya samar da motocin ne domin jigilar sama da manoma 10,000 zuwa gonakinsu a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng