"Babu Lokacin Murna": Shugaba Tinubu Ya Aike da Zazzafan Gargadi Ga Hafsoshin Tsaron Najeriya
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya faɗa wa hafsoshin tsaron ƙasar nan cewa ba ya wasa da rahotannin sirri ko kaɗan
- Tinubu ya ja kunnen hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri cewa gwamnatinsa ba zata lamurci gazawa ba
- Ya ce ya zama wajibi rundunar sojin Najeriya ta kawar da dukkan matsalolin tsaron da suka zame wa kasar nan karfen ƙafa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi manyan hafsoshin tsaron kasar nan da cewa gazawa ba zabi bane a gwamnatinsa.
Shugaban ƙasar ya kuma shaida musu cewa ba ya ɗaukar rahotannin bayanan sirri da wasa.
Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin hulɗa da jama'a, Fredrick Nwabufo, shi ne ya wallafa sanarwan a shafinsa na manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce dole ne sojojin kasar su cimma burinsa na tabbatar da dorewar samar da ganga miliyan biyu na danyen mai a kowace rana.
Shugaban ƙaaa ya kuma bukaci rundunar sojin kasar da su tabbatar da cewa an samu cikakkiyar nasara kan dumbin barazanar tsaro da ta dabaibaye Najeriya.
Tinubu ya ja kunnen hukumomin tsaro
Ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri a fadar shugaban ƙasa ranar Jumu'a, 5 ga watan Janairu.
A wurin taron majalisar tsaro a Villa, shugaba Tinubu ya ce:
"Kuna samun nasarori masu yawa kuma ƴan Najeriya sun shaida amma kuskuren da za a iya kaucewa kamar wanda ya auku a Kaduna ba zan yarda da shi ba, a kiyaye.
"Na gamsu da haɗin kan da aka samu tsakanin hukumomin tsaro a yan watannin nan amma har yanzu babu ƙofar yin murna har sai mun ga bayan lamarin, sojojin mu sun koma gida.
"Bana wasa da bayanan sirri, ku sani ina da idanuwan gani da yawa. Sojojin ruwa da sauran hukumomin ƙawayenta dole su tashi tsaye haiƙan domin amfanar ƴan Najeriya. Gazawa ba zaɓi bane a gwamnatina."
Majalisar dattawa ta fayyace gaskiya
A wani rahoton kuma Majalisar dattawan ta musanta rahoton cewa sanatoci sun karbe tallafin kayan abinci na N200m kowanensu daga Tinubu domin rabawa talakawa.
Shugaban kwamitin watsa labarai, Adeyemi Adaramodu, ya karyata jita-jitar wacce ta fito daga bakin hadimin shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng