Tsadar Kudin Hajji: Ƙungiyar ANA Ta Ɗauki Matakan Nemawa Maniyyata Sauƙin Zuwa Sauke Farali a 2024

Tsadar Kudin Hajji: Ƙungiyar ANA Ta Ɗauki Matakan Nemawa Maniyyata Sauƙin Zuwa Sauke Farali a 2024

  • Wata kungiya mai rajin kawo cigaba a Arewa (ANA) ta yunkuro domin ganin maniyyata sun samu saukin zuwa Saudiyya sauke farali a 2024
  • Hakan na zuwa ne yayin da maniyyata ke fuskantar kallubale da dama a bana da suka shafi farashin kudin kujera, karancin lokacin biyan kudin da sauransu
  • Sanata Ahmad MohAllahyidi, shugaban ANA tare da sauran shugabannin kungiyar sun gudanar da bincike tare da mika shawarwari ga Hukumar NAHCON da nufin samarwar maniyyata sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Kungiyar Arewa New Agenda (ANA) karkashin jagorancin Sanata Ahmad Abubakar MoAllahyidi ta kaddamar da wani gangami da nufin saukakawa yan Najeriya zuwa Hajji a 2024.

Wannan gangamin zai duba muhimman batutuwa da suka shafi kudi da damar zuwa sauke farali, tare da bada shawarwari da za su saukaka tsadar kudin da maniyyata ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Sanata ya yunkuro don ganin an rage wa maniyyata kudin hajji
Sanata Ahmad Abubakar MoAllahyidi, shugaban ANA, tare da shugabannin kungiyar yayin mika rahotonsu a ofishin NAHCON da ke Abuja.
Asali: UGC

A cewar shugaban ANA, Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) tana goyon baya wannan gangamin dari bisa dari, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyoyin da ANA za ta bi don cimma manufofinta

Wannan gangamin na ANA ya kunshi tuntubar muhimman masu ruwa da tsaki daga yankunan Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Abuja, tare da tattaunawa da jagororin addini, Hukumomin alhazai na jihohi domin magance matsalolin da ke addabar alhazai gabanin cikar wa’adin ranar 31 ga watan Disamban 2023 na rufe biyan kudin aikin Hajjin 2024.

Gangamin na ANA zai tunkari kallubale da dama da suke shafi saukaka kudin hajji, samar da masauki kusa da Harami, tsarin ciyarwa, kudin jirgi, da kudin hidima, wadanda duk sun bada gudunmawa wurin tsadar kudin aikin hajjin na bana.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rantsar da sabbin ciyamomi 38 da mataimakansu, sun kama aiki gadan-gadan

Masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwarsu yayin tattaunawa, musamman game da damfara da ake yi wa maniyyata, jinkirin isar da sakonni da karancin wayar da kan al’ummar karkara dangane da sabbin ka’idoji da wa’adin biyan kudin Hajjin 2024.

Bincike ya nuna wasu yankuna sun cika kasonsu na Hajji, wasu kuma na fuskantar kallubale saboda jinkirin yanke shari'a a kotu da rashin cika wasu alkawurra. An bada shawarwarin tsawaita wa'adin biyan kudin hajji tare da yin rangwamen kudin kujera.

Shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka bayar kan Hajjin Bana

Yankin Arewa ta Tsakiya ta koka kan rashin ingantaccen bayanai tare da bada shawarar mayar da hankali wurin gangamin ilimantarwa ga maniyyata da mutanen karkara, a cewar rahoton Leadership.

Masu ruwa da tsaki sun yi kira a cigaba da wayar da kai, hadin gwiwa da cibiyoyin hada-hadar kudi don magance matsalar biyan kudi, da kuma kira ga gwamnatoci su rage kudin hajji, a magance matsalolin da suka shafi zamba, inganta gudanarwa, da bullo da tsarin adashin hajji da wuri.

Kara karanta wannan

Kano: Babban Malami ya faɗi mafita 1 tak da ta rage wa Gwamna Abba gabanin hukuncin Kotun Koli

Jami’an gwamnati a jihohi daban-daban da suka hada da Kano, Kebbi, Abuja, Zamfara, Kwara, da Nasarawa, sun bayyana kwarin guiwar game da matakan da gwamnatocinsu suka dauka na ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2024, tare da tabbatar da aniyarsu ta magance kallubalen rashin iya biyan kudin kujeru.

Sanata MohAllahyidi ya mika godiyarsa bisa goyon baya daga Hukumar Hajji ta Kasa da jihohi, inda ya yaba da kokarin da suke yi na saukaka Hajjin 2024 ga musulmin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164