Asiri Ya Fara Tonuwa: An Kama Mutum 8 da Ake Zargi da Hannu a Kisan Bayin Allah Sama da 150

Asiri Ya Fara Tonuwa: An Kama Mutum 8 da Ake Zargi da Hannu a Kisan Bayin Allah Sama da 150

  • Dakarun yan sanda sun kama mutum 8 da ake zargin suna da alaƙa da kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin jihar Filato
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na jihar, DSP Alfred Alabo, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Jumu'a
  • Tun bayan kisan rayuka sama da 150, hukumomin tsaro suka sha alwashin daƙile faruwar makamancin haka a faɗin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Filato ta bayyana cewa ta kama mutum 8 da take zargin suna da hannu a kashe-kashen da aka yi kwanan nan a jihar Filato.

Rundunar ta ce dakarun ƴan sanda sun kama mutanen da ake zargin suna da alaka a kashe-kashen wanda aka yi a kauyukan kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi.

Kara karanta wannan

Dakarun ƴan sanda sun kama mutane 2,931 bisa zargin aikata laifuka fiye da 3 a jihar Kano

Sufetan yan sandan Najeriya, IGP Kayode.
An Kama Mutum 8 Masu Hannu a Kisan Bayin Allah 195 a Jihar Filato Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sama da mutum 150 ne aka tabbatar sun mutu a lamarin yayin da gidaje da yawa suka ƙone.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kimanin kauyuka 23 na ƙaramar hukumar Bokkos ne aka kai wa hari a ranar jajibirin Kirsimeti, inda mahara suka ƙona daruruwan gidaje.

Mun kama mutane 8 da ake zargi - Yan sanda

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ne ya bayyana kama waɗanda ake zargin ranar Jumu'a, 5 ga watan Janairu, 2024.

Tun bayan abin da ya faru, hukumomin tsaro da suka haɗa da rundunar sojojin ƙasa, sojojin sama da na ruwa da rundunar ƴan sanda suka sha alwashin kawo ƙarshen lamarin.

Hukumomin tsaron sun lashi takobin daƙile ci gaba da faruwar wannan kashe-kashe na ba gaira babu dalili da kuma magance kai wa juna hari tsakanin kauyukan manoma da makiyaya.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Sai dai duk da cewa an girke jami’an tsaro a ƙauyukan da lamarin ya shafa, ana samun karin kashe-kashe a ɓoye kusan kowace rana.

Ko a kwanan nan, rahoto ya nuna an kashe wani babban limamin masallacin Jumu'a da wani ɗan acaɓa duk a yankin Bokkos, The Cable ta ruwaito.

Mata Sun Banka Wa Gidan Basarake Wuta a Bokkos

A wani rahoton na daban Tashin hankali yayin da wasu mata da suka fito zanga-zanga suka banka wa gidan hakimin Bokkos wuta a jihar Filato.

Bayanai sun nuna cewa matan sun yi haka ne domin nuna ɓacin ransu kan kama waɗanda ake zargi da kashe-kashen kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262