Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade a Manyan Hukumomi 2 Bayan Sallamar Masu Rike da Kujerun
- Bayan sallamar manyan daraktoci a hukumomin NPA da NIMASA, Shugaba Tinubu ya nada sabbin jini
- Tinubu ya sanar da nadin nasu ne a yau Alhamis 4 ga watan Janairu ta bakin hadiminsa, Ajuri Ngelale
- Ngelale a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis 4 ga watan Janairu ya ce nadin zai fara aiki nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sabbin nade-nade a hukumomin NPA da NIMASA.
Tinubu ya bayyana sunayen wadanda aka nadan ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale.
Yaushe Tinubu ya yi sabbin nade-naden?
Ngelale a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis 4 ga watan Janairu ya ce nadin zai fara aiki nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajuri ya ce Tinubu ya nada Vivian Edet a matsayin babbar darakta a bangaren kudade da gudanarwa, cewar TheCable.
Har ila yau, Tinubu ya nada Olalekan Badmus a matsayin babban daraktan bangaren albarkatun ruwa da ayyuka a hukumar NPA.
Yayin da aka nada Ibrahim Abba Umar babban daraktan bangaren gyare-gyare da fasaha dukkansu a hukumar NPA.
Sauran wadanda aka nadan a hukumar NIMASA
Sai kuma hukumar NIMASA, daraktocin sun hada da:
Mista Jibril Abba, babban daraktan bangaren albarkatun ruwa da ayyuka sai kuma Mista Chudi Offodile, babban daraktan kudade da gudanarwa a NIMASA.
Har ila yau, akwai Injiniya Fatai Taye Adeyemi wanda shi ne babban daraktan ayyukan a hukumar NIMASA.
Tinubu ya bukaci dukkan sabbin nade-naden da su yi aiki tukuru inda ya ce ya yi imanin cewa su na da kwarewar aiki shiyasa ya basu mukaman.
TUC ta tura bukatu 10 ga Tinubu a 2024
A wani labarin, Kungiyar TUC ta lissafo wasu bukatu guda 10 ga Shugaba Bola Tinubu yayin da aka shiga sabuwar shkarar 2024.
Kungiyar ta fitar da sanarwar ce da sa hannun shugabanta, Festus Osifo da kuma sakatarenta, Nuhu Toro a yau Alhamis 4 ga wata Disamba.
Kungiyar har ila yau, ta gargadi Tinubu da ya tabbatar ya cika dukkan bukatun don kauce wa matsala.
Asali: Legit.ng