Daga Shiga 2024 Gwamnatin Bola Tinubu Zata Ƙara Farashin Man Fetur a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Daga Shiga 2024 Gwamnatin Bola Tinubu Zata Ƙara Farashin Man Fetur a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin mai na ƙasa NNPCL ta musanta raɗe-raɗin ana shirin ƙara farashin litar man fetur
  • A wata sanarwa da kamfanin mai ya fitar ranar Laraba, ya buƙaci ƴan Najeriya su kwantar da hankulansu domin labarin ƙarin ba gaskiya bane
  • Wannan na zuwa ne bayan ƴan kasuwar mai sun yi zargin cewa har yanzu FG na biyan kuɗin tallafi shiyasa farashi bai ƙaru ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce babu wani shiri a ƙarƙashin ƙasa na kara farashin man Premium Motor Spirit (PMS) wanda aka fi sani da fetur.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kamfanin NNPCL ya wallafa a shafinsa na manhajar X, wanda aka fi sani da Tuwita ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Hukumar NAHCON ta dauki sabon mataki bayan wa'adin biyan kudin aikin Hajjin 2024 ya kare

NNPCL ya musanta kara farashin litar mai.
Babu zancen kara farashin litar man fetur a Najeriya, im ji kamfanin NNPCL Hoto: NNPCL
Asali: Facebook

Da yawan ƴan Najeriya sun shiga fargaba biyo bayan ikirarin manyan ƴan kasuwar man fetur cewa ya kamata a ce farashin lita ya tashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ƴan kasuwar mai, duba da yadda kuɗin Amurka Dala ke ƙara tumurmusa kuɗin Najeriya, kamata ya yi litar fetur ta kai N1,200 idan har an tsige tallafi gaba ɗaya.

Shin menene gaskiya kan batun tsadar fetur?

A wata sanarwa da shugaban sashin yaɗa labarai na kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya fitar ranar Laraba, ya musanta raɗe-raɗin ƙara tsadar man fetur a ƙasar nan kusa.

Ya kuma yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su yi fatali da duk wata jita-jita cewa nan gaba kaɗan zasu ga farashin da suke sayen litar fetur ya ƙaru.

Soneye ya tabbatar wa al'ummar Najeriya cewa babu wani shiri na sake duba da ƙara farashin man fetur a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“NNPC Ltd na tabbatar wa da jama’a cewa babu wani karin kudin da za a yi na farashin man Motoci wanda aka fi sani da fetur.
"Ana shawartan masu ababen hawa da su guji haɗa cunkoso da layin siyan mai a gidajen mai saboda a halin yanzu akwai wadatar Fetur a duk faɗin ƙasar nan."

Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Sarakuna 6

A wani rahoton kuma Gwamna Ademola Adeleke ya naɗa sabbin sarakuna shida kuma ya ɗaga darajar wasu guda 11 a jihar Osun.

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Kolapo Alimi, ne ya tabbatar da haka bayan taron majalisar zartarwa ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262