Digirin Bogi: Ina Cikin Damuwa Game Da Tsarona, Dan Jaridar Da Ya Saki Rahoton 'Digiri Dan Kwatano'

Digirin Bogi: Ina Cikin Damuwa Game Da Tsarona, Dan Jaridar Da Ya Saki Rahoton 'Digiri Dan Kwatano'

  • Umar Audu, dan jarida da ke aiki da Daily Nigerian wanda ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano' ya nemi jami'an tsaro su tabbatar da tsaronsa, yana mai cewa yanzu ba ya shiga mutane sosai
  • Audu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba 3 ga watan Janairun 2024
  • Dan jaridar mai bincike ya ce kawo yanzu bai samu wata barazana ba amma yan uwa da abokansa suna nuna damuwa kan lafiyarsa saboda bazuwar rahoton

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Dan jaridan Najeriya mai bincike kwa-kwaf, Umar Audu, ya bayyana cewa yana fargabar lafiyarsa bayan sakin rahoton bincike inda ya fallasa wasu masu bai wa mutane digirin bogi a Togo da Jamhuriyar Benin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bukaci naira miliyan 60 fansar yara 6 da suka sace a Abuja

Idan za a iya tunawa, dan jaridar mai bincike da ke aiki da Daily Nigerian, ya rahoto cewa a yan kwanakin nan ya samu digiri cikin makonni shida a irin wadannan jami'o'in kuma ya shiga sansanin bai wa masu yi kasa hidima horaswa ya samu satifiket.

Umar Audu
Ina rokon jami'an tsaro su tabbatar da tsaron lafiyata, dan jarida Umar Audu. Hoto: @Theumar_audu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan jaridar ya samu satifiket da takardar sakamakon yin kwasa-kwasai daga jami'ar 'Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, Cotonou, Jamhuriyar Benin' bayan makonni shida kacal, rahoton Vanguard.

A hirar da aka yi da shi da Channels Television a ranar Laraba, ya ce abin damuwa ne yadda jami'an tsaro a Najeriya ba su bai wa yan jarida irin kwarin gwiwar yin ayyukansu ba tare da tsoron tsangwama ba.

Da mai gabatar da shirin ya masa tambaya idan kawo yanzu an masa barazana bayan fitowar rahoton, ya ce duk da cewa bai riga ya samu wata barazana ba, ba ya shiga cikin al'umma domin dole ya bai wa tsaronsa muhimmanci.

Kara karanta wannan

Bayan cewa bai son a kai masa ziyara, Buhari ya yi kyautar galleliyar mota ga dan a mutunsa

Ina bukatar gwamnati ta tabbatar da tsaron lafiyata, Audu

"Yan uwa da abokaina da dama suna nuna damuwarsu kan lafiyata. Suna nuna damuwa sosai, kuma a matsayina na dan jarida, na yi imanin ya kamata a kyalle ni in yi aikina ba tare da barazana ko tsangwama ba.
"Wannan lamarin ya nuna irin yanayin da muka zama ciki, inda ya kamata yan jarida su iya yin aikinsu cikin zaman lafiya kuma a tabbatar da tsaronsu.
"Ina son amfani da wannan damar in yi kira ga mahukunta su tabbatar da tsaron lafiyata, duk da yanzu ba cikin hatsari na ke ba. Sai dai, ban da tabbas kan abin da zai faru gaba, domin ina ta yin hira da yan jarida kuma rahoto na ya bazu sosai ba tare da wani barazana ba kawo yanzu.
"Ina fara gwamnati za ta cigaba da sa ido, kuma idan akwai wani barazana, zan sanar da su nan take domin su tabbatar an bani tsaron da ya kamata."

Kara karanta wannan

Kotu a Kano ta bada umurnin kama jami’in kwastam kan kin amsa ‘sammacin da aka tura masa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164