EFCC Ta Rike Naira Biliyan 30 Na Gwamnati da Aka Samu Cikin Asusun Wasu Mutane

EFCC Ta Rike Naira Biliyan 30 Na Gwamnati da Aka Samu Cikin Asusun Wasu Mutane

  • Binciken jami’an EFCC ya kai ga wasu makudan biliyoyi da ake nema bayan sun bar asusun gwamnati
  • Hukuma ta tsare wadannan kudi har Naira biliyan 30 a yayin da ake bincike a kan zargin badakalar NSIPA
  • EFCC ta zauna da wasu jami’an hukumar NSIPA domin jin gaskiyar inda aka karkatar da wasu N44bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta ci karo da N30bn daga cikin N44bn da aka motsa da su daga NSIPA.

The Nation ta ce ana zargin an karkatar da biliyoyin kudi daga hukumar da aka kafa domin ta taimakawa marasa galihu.

EFCC.
EFCC ta na binciken NSIPA Hoto: Getty, Tori.ng
Asali: Getty Images

EFCC: N44bn sun bace daga NSIPA?

Ana zargin wasu N44bn sun yi kafa a hukumar NSIPA wanda hakan ya jawo EFCC ta ke binciken kwa-kwafa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: Ana barazanar cafko Ministar Buhari a kan yi wa EFCC taurin kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce wadannan kudi sun burma asusun daidaikun mutane da wasu kamfanoni da aka fake da sunansu a kasar.

A dalilin haka jami’an EFCC su ke ta yin bincike na musamman ta karkashin kasa domin su iya gano inda aka boye kudin.

Jami'an NSIPA a hannun EFCC

Shugabar NSIPA da aka dakatar, Halima Shehu ta shafe tsawon awanni hudu a ranar Laraba tana ta amsa tambayoyi a EFCC.

EFCC ta kuma cafke tsohon darektan kudi da tattalin arziki na hukumar NSIPA a Najeriya watau Mista Bwai Adamu Hamza.

Bwai Hamza ya yi ritaya daga hukumar gwamnatin tarayyar ne a watan Disamba.

Halima Shehu da Bwai Adamu Hamza sun fuskanci wasu jami’an bincike na musamman a game da zargin da ke wuyansu.

Hukumar EFCC ta rike N30bn

Bayan an bibiyi kudin da ake nema, an yi nasarar gano inda wasu su ka shiga, kuma har an iya rike N17bn a asusu dabam-dabam.

Kara karanta wannan

Alumundahar N37bn: Ministan gwamnatin Buhari Sadiya Farouq ta yi biris da gayyatar EFCC

A cikin awanni 24, hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta gano karin N13bn, yanzu an samu an rike akalla N30bn kenan.

Masu kudin Afrika a 2024

Kamar kowace shekara, Aliko Dangote da wasu tsirarun ‘yan Afrika na cikin Attajiran Duniya, an ji labari hakan abin yake bana.

AbdulSamad Rabiu, Mike Adenuga da Nassef Sawris sun ba Naira tiriliyan 14 baya yanzu idan har lissafin mujallar Forbes ya tabbata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng