“Ba Zan Ci Gaba Haka Ba a 2024”: Matashi Ya Juya a Hanyarsa Ta Zuwa Aiki, Ya Ajiye Aikin

“Ba Zan Ci Gaba Haka Ba a 2024”: Matashi Ya Juya a Hanyarsa Ta Zuwa Aiki, Ya Ajiye Aikin

  • Wani dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a dandalin X bayan ya bada labarin yadda ya ajiye aikinsa kwatsam a sabuwar shekarar nan
  • A cewarsa, ya kasance a tashar mota a hanyarsa ta zuwa wajen aiki lokacin da wannan tunani ya hau kansa na ajiye aiki nan take
  • Mutane sun nuna goyon bayansu ga wannan shawara da ya yanke, inda suka taya shi da addu'an samun nasara a sabuwar hanyar da ya dauka

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani dan Najeriya ya bayyana yanayi mai ban mamaki da ya bi wajen ajiye aikinsa a farkon sabuwar shekarar nan.

Matashin mai suna @Delecredible a dandalin X ya ce yana tsaye a tashar mota a hanyarsa ta zuwa wajen aiki ne lokacin da ya gane cewa wannan ba ita ce hanyar da yake son bi ba a 2024.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Abu 1 da Ba Zai Yi Tasiri ba a 2024

Dan Najeriya ya yanke shawarar ajiye aiki
“Ba Zan Ci Gaba Haka Ba a 2024”: Matashi Ya Juya a Hanyarsa Ta Zuwa Aiki, Ya Ajiye Aikin Hoto: @delecredible/X
Asali: Twitter

Mutumin da ya ajiye aiki a tashar mota ya yi fice

A cewarsa, nan take ya yanke shawarar da ta dace a tashar motar na kada ya kara zuwa wajen aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Yanayin yadda na ajiye aikina a safiyar nan akwai ban dariya, na isa tashar mota na nufi wurin aiki sai kuma na ji kamar ba wannan ne abin da nake so in yi da rayuwata a wannan shekara ba."

Jama'a sun yi martani da addu'o'i tare da marawa mutumin da ya ajiye aiki baya

Mutane sun yi gaggawar nuna goyon baya da fatan alheri ga mutumin bayan jin labarinsa.

@johnpraise_ ya ce:

"Ina addu'ar Allah ya sa ka sami haske da aikin da kuke so da gaske."

@daisyiv_ ya mayar da martani:

"Ina addu'a Allah ya yi maka jagora ya kuma kare shawarar da za ka yanke a gaba, watakila na yi irin haka nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

"Ka nemi mata": Maratanin jama'a yayin da Dino Melaye ya koka da rayuwar kadaici, bidiyon ya yadu

@AwwalNdako ya ce:

“Don Allah ka yi shi a hukumance. Kuma da fatan Allah Ya sa ka yi nasara a ayyukanka na gaba”.

@shopfromros ya mayar da martani:

“Ni kenan a shekarar da ta gabata. Babu shiri, babu tanadi. Na yi shirin aiki, ina fitowa waje na ce "a'a, zan wuce."

Budurwa ta sille tsoho soso da sabulu

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya a dandalin X ta nuna gajiyawarta a kan abubuwan da wani dattijo ke yawan yi mata.

Matashiyar mai suna @DeejustDee ta dauki hotunan sakonnin da yake ta aika mata, tare da baje kolin maganganunsa da kuma kin mutunta iyakokinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng