Miyagu Sun Harbe Babban Limamin Masallacin Jumu'a da Ɗan Acaɓa a Filato

Miyagu Sun Harbe Babban Limamin Masallacin Jumu'a da Ɗan Acaɓa a Filato

  • Wasu tsageru sun halaka babban limamin Masallacin Jumu'a da wani ɗan acaba a sabon harin da aka kai jihar Filato
  • Shugaban ƙungiyar Fulani GAFDAN, Garba Abdullahi, ya ce tuni aka sanar da jami'an tsaro abin da ya faru don ɗaukar mataki
  • Wannam hari na zuwa ne mako ɗaya bayan hare-hareen da aka kai kauyuka sama da 20 a karamar hukumar Bokkos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - An shiga yanayin tashin hankali a jihar Filato yayin wani sabon hari da aka kai ya yi ajalin manyan mutane ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2023.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa maharan sun kashe babban limamin masallacin Jumu'a na kauyen Ndun da ke ƙaramar hukumar Bokkos, Malam Muhammad Sani Idris.

Kara karanta wannan

DHQ: Duk da kashe bayin Allah 195, Sojoji sun dakile munanan hare-hare a ƙauyuka 19 a Filato

Gwamna Celeb Mutfwang na jihar Filato.
An Kashe Babban Limamin Masallacin Jumu'a da Wani Dan Okada a Sabon Harin Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Haka nan kuma sabon harin ya yi ajalin wani ɗan acaba da aka bayyana sunansa da, Muhammad Gambo, duk a ƙauyen na jihar Filato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar Fulani 'the Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN), Garba Abdullahi, shi ne ya tabbatar da haka ga ƴan jarida ranar Laraba.

A cewar Abdullahi, dan uwa ga babban Limamin, Salisu Muhammad Sani Idris, ya samu rauni a harin, kuma yanzu haka yana jinya a asibitin Dung da ke garin Bokkos.

Ya ƙara da cewa tuni aka sanar da dakarun tsaro da ke Bokkos abin da ya faru domin ɗaukar matakin da ya dace a kan lokaci, rahoton The Nation.

Wannan kisan na makiyayan biyu ya zo ne mako guda bayan hare-haren da aka kai a kauyuka kusan 23 na karamar hukumar Bokkos, inda aka kashe sama da mutane 150.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Yadda aka ƙashe babban limamin Jumu'a

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, shugaban GAFDAN ya ce:

"An farmaki babban limamin da kaninsa ranar Litinin bayan sun isa ƙauyen domin kwashe ragowar kayansu da suka rage bayan hare-haren kwanakin baya, wanda aka ƙona mana gidaje.
"Saboda haka sun je garin ne domin ganin ko zasu iya kwaso sauran kadarorin su kwatsam aka kai masu hari. Miyagun sun kashe limamin amma ƙaninsa ya tsira da raunin wuƙa.
“Na biyu da aka kashe, Muhammed Gambo, dan okada kuma mamban mu, an kashe shi ne a ranar Litinin a kusa da Kasuwar Bokkos yayin da ya kawo fasinja zuwa unguwar."

Yayin da aka tuntubu kakakin rundunar Operation Safe Haven, Kaftin Oya James, da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Filato, DSP Alabo Alfred, babu wanda ya amsa.

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Abuja da Neja

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a birnin tarayya Abuja da jihar Neja da ke maƙotaka, sun kashe mutane huɗu.

Rahotanni sun nuna cewa yayin hare-haren a lokuta daban-daban, yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu mutane 39.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262