Kamfanin Allura da Sirinji Mafi a Girma a Afirka Ya Rufe Ofishinsa Na Najeriya, Ya Faɗi Dalili 1 Tak
- Kamfanin da ke kera Allura da sirinji a Najeriya ya dakatar da ayyukansa saboda taɓarɓarewar harkokin kasuwanci
- A wata takarda da ya aike wa ma'aikatansa, kamfanin ya ce ɗaukan wannan matakin ya zama tilas duba da halin da ya shiga
- Tsohon mstaimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da wannan kamfani mafi girma a 2017
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Kamfanin kera allura da Sirinji 'Jubilee Syringe Manufacturing' da ke Owa, ƙaramar hukumar Onna a jihar Akwa Ibom, ya dakatar da aiki a Najeriya.
Kamfanin mafi girma a faɗin Nahiyar Afirka ya ce ya ɗauki wannan matakin ne, "saboda matsi da wahalar kasuwanci wanda ba a taɓa zato ba da ya shafi ayyukan mu."
Kamfanin wanda ake kyautata zaton shi ne kamfani mafi girma na masana'antar sirinji a Afirka, tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ne ya kaddamar da shi a 2017.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Koda yake ya daina ƙera sabbin sirinjai watanni da yawa da suka gabata, a ƙarshe ya ba da sanarwar rufe ayyukansa gaba ɗaya a ranar 31 ga Disamba, 2023.
Ya bayyana cewa dole ne ya gaggauta aiwatar da matakan wucin gadi don tabbatar da dorewar kamfanin, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.
Kamfanin ya aike da saƙo ga ma'aikatansa
Haka nan kamfanin ya tabbatar da tashi daga Najeriya a wata takarda da ya aike wa ma'aikatansa, wanda kwafinta ya shiga hannun ƴan jarida.
Wani ɓangaren takardar da kamfanin ya turawa ma'aikatan ya ce:
"Muna fatan wannan sakon zai same ku cikin koshin lafiya. Mun rubuto muku wannan takarda don sanar da matakin da kamfani ya ɗauka saboda matsalolin da suka shafi harkokin kasuwancinmu.
"Bayan yin la'akari da nazari a tsanake kan yanayin kasuwancinmu na yanzu, muna baƙin cikin sanar da ku cewa dole ne mu ɗauki wasu matakan wucin gadi don tabbatar da dorewar kamfanin.
"Bisa rashin sa'a waɗannan matakai sun kunshi dakatar da ayyukanku na wucin gadi daga ranar 1 ga watan Janairu, 2024. Kalubalen kasuwanci da muka sami kanmu a ciki ne ya tilasta mana ɗaukar waɗannan matakai masu wahala.
"Don Allah muna rokon ku mayar da duk kayan kamfanin da ke hannun ku. Mun gode da kuka fahimce mu a irin wannan yanayi mara daɗi"
'Najeriya ba zata warke ba sai da taimakon Allah'
A wani rahoton na daban An shawarci Bola Ahmed Tinubu ya koma cikin Alqur'ani mai girma akwai maganin dukkan matsalolin Najeriya.
Farfesa Abdullahi El-Okene, shugaban ƙungiyar IOTB ne ya aike da saƙo ga shugaban ƙasa a wurin wani taro a Abuja.
Asali: Legit.ng