Ana Dab da Yanke Hukunci Gwamna Abba Ya Nemi Wata Muhimmiyar Bukata 1 Daga Attajiran Kano

Ana Dab da Yanke Hukunci Gwamna Abba Ya Nemi Wata Muhimmiyar Bukata 1 Daga Attajiran Kano

  • A ƙoƙarin ganin al'ummar jihar Kano sun samu ayyukan cigaba, Gwamna Abbba ya jawo hankalin attajiran jihar
  • Gwamnan ya yi kira ga masu hannu da shuni da su haɗa kai da gwamnatinsa wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al'umma
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa ya kamata masu hannunda shunin sunyi koyi da takwarorinsa na sauran sassan ƙasar nan wajen inganta rayuwar al'ummar su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da su haɗa kai da gwamnatinsa wajen gudanar da ayyukan da za su yi tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnan ya yi wannan roƙo ne a wani shiri na musamman na sabuwar shekara da aka haska daga ofishinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa ta Tsakiya sun fadi abu 1 da FG za ta yi ka hare-haren Plateau

Gwamna Abba ya yi kira ga masu hannu da shuni
Gwamna Abba ya bukaci attajiran Kano su bada gudunmawa wajen aiwatar da ayyukan cigaba a jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar da ɗumbin attajirai da masu sana’o’in hannu waɗanda taimakonsu zai taimaka matuka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa akwai bukatar a haɗa ƙarfi da ƙarfe domin inganta rayuwar masu ƙaramin ƙarfi a jihar, rahoton Trust Radio ya tabbatar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa tana da kyakkyawan tsari a fannonin asusun tallafawa ilimi, asusun tsaro da asusun tallafawa jama’a, sannan gudunmawa daga irin waɗannan mutane za ta taimaka wajen gudanar da ayyuka sosai.

Gwamna Abba ya jawo hankalin attajiran Kano

Gwamnan ya ba da misali da wasu sassan ƙasar nan inda masu hannu da shuni suka mayar da al’adar aiwatar da ayyuka da ɗaukar nauyin shirye-shiryen da za su kyautata al'ummar su.

A kalamansa:

"Lokacin da na zo ofis, ina sa ran irin waɗannan ƴan kasuwa za su tunkare mu da gudummawar su wacce za a yi amfani da ita yadda ya dace wajen aiwatar da ayyuka da nufin inganta rayuwar al’umma amma hakan bai faru ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya bayyana dalili 1 da yasa ya amince da yin sulhu a rikicinsa da Wike

"Ina so in yi amfani da wannan dama domin in yi kira gare su da su yi koyi da takwarorinsu na sauran sassan ƙasar nan ta hanyar ba da goyon bayansu wajen ganin jiharmu ta zama wuri mafi kyau ga al’ummarmu."

Ma'aikata da Ƴan Fansho Za Su Samu Ƙarin Kuɗi a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano za ta yi wa ma'aikata da ƴan fansho ƙarin kuɗi a jihar, saboda tsige tallafin man fetur.

Gwamnan zai fara biyan ma'aikata ƙarin N20,000 a albashinsu daga watan Disamban 2023 domin su rage raɗaɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng