Gwamna Abba Ya Kori SSG Abdullahi Baffa Bichi? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna Abba Ya Kori SSG Abdullahi Baffa Bichi? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi magana kan batun korar sakataren gwamnatin jihar daga mukaminsa
  • Rahotanni sun yaɗu kan cewa gwamnan ya samu saɓani da Abdullahi Baffa Bichi wanda ya kai ga korar SSG ɗin daga muƙaminsa
  • Sai dai, gwamnan ya musanta hakan inya bayyana cewa har yanzu Baffa na nan daram a kan muƙaminsa kuma ba su samu saɓani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa na cewa ya kori sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi bayan wata rashin fahimta da suka yi da shi.

A halin yanzu SSG yana ƙasar Saudiyya domin neman lafiya yayin da aka umurci shugaban ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa ya riƙe ofishin a matsayin muƙaddashinsa.

Kara karanta wannan

Digirin bogi na Kwatano: Ban taba shiga aji ba N600k kawai na kashe, dan jarida

Gwamna Abba ya yi magana kan korar SSG
Gwamna Abba ya musanta korar Abdullahi Baffa Bichi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tun daga wannan lokacin ne aka riƙa yaɗa labarai a kafafen sada zumunta musamman na ƴan jam’iyyar adawa cewa sun samu ɓaraka bayan da aka kama wani babban mataimaki na musamman ga gwamnan yana ɗibar kayan abincin da za a rabawa marasa galihu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi amannar cewa SSA ɗin ya fito ne daga sashin SSG kuma cafke shi ya sanya ya kai ƙorafi ga maigidansa wanda rahotanni suka ce ya kai kuka ga gwamnan.

Me Gwamna Abba ya ce kan korar Bichi?

Sai dai, da yake mayar da martani kan batun, gwamnan a ranar Talata, jim kaɗan bayan rantsar da sabbin manyan sakatarorin da ya naɗa, ya ce bai kori SSG ba, kuma ba su da wata rashin fahimta da shi, cewar rahoton Daily Trust.

A kalamansa:

"Wani yana cewa yana wajen lokacin da muka yi faɗa. Wannan shine mafi girman jahilci amma muna roƙon Allah ya yaye musu."

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya bayyana dalili 1 da yasa ya amince da yin sulhu a rikicinsa da Wike

"Har yanzu SSG yana nan a matsayinsa kuma muna godiya a gare shi da irin gudunmawar da ya bayar da fatan idan ya dawo ya cigaba."
"Yayin da shugaban ma’aikata ke riƙe da muƙamin a rashin (SSG) ba yana nufin an kore shi ba. Ba mu sauke shi daga muƙaminsa ba. inji gwamnan.

NNPP Ta Musanta Yarjejeniya da APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta musanta cimma yarjejeniya da jam'iyyar APC kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.

Rahotanni sun yaɗu kan cewa ɓanngarorin biyu sun cimma yarjejeniya yayin da ake jiran hukuncin da kotun ƙoli za ta yanke kan shari'ar zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng