Gwamnan Arewa Ya Ayyana Zaman Makokin Mako 1 a Jiharsa Kan Kisan da Aka Yi Wa Bayin Allah
- Gwamna Caleb Mutfwang na Filato ya ayyana zaman makokin mako guda domin jimamin wadanda aka kashe a hare-haren yan bindiga a jihar
- Yan bindiga sun farmaki jihar ta arewa ta tsakiya inda suka halaka mutum sama da dari da lalata kaya na miliyoyin naira
- Gwamna Mutfwang ya kuma bayar da umurnin sauke tutoci zuwa rabi yayin zaman makokin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Filato ta ayyana kwanaki takwas domin zaman makokin bayin Allah sama da 100 da suka rasa rayukansu a hare-haren yan bindiga a wasu garuruwan jihar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an fara zaman makokin a ranar 1 ga watan Janairu kuma za a gama a ranar 8 ga watan Janairu.
Hare-haren da ya gudana a kananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos da Mangu ya fara a ranar jajiberin Kirsimeti kuma ya ci gaba har ranar Kirsimeti, inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi na miliyoyin naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake ayyana ranakun zaman makokin a ranar Litinin, 1 ga watan Janairu a jawabin sabuwar shekara, Gwamna Caleb Mutfwang ya ce za a sauke tutoci zuwa rabi yayin zaman makokin.
Gwamna Mutfwang ya yi kira ga malaman addini
Kan haka, ya yi kira ga malaman musulunci da su sadaukar da Juma'a, 5 ga watan Janairun 2024 sannan malaman kirista suma su yi amfani da Lahadi, 7 ga watan Janairu don yin addu'o'i na musamman na dorewar zaman lafiya a jihar.
"Bari na sake amfani da wannan kafar domin jajanta wa masoyana mutanen Filato kan wadannan kashe-kashe, musamman garurwan da abun ya shafa da kuma iyalan wadanda suka mutu. Zuciyata na tare da ku kuma na tabbata cewa iyalina, ni da gwamnati gaba daya muna jin bakin cikin da kuke ji.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, amma za mu ci gaba da hada kai da gwamnatin tarayya don kawo karshen wadannan bala’i da kuma kawo tallafi ga mutanen da garuruwan da abin ya shafa.
“A matsayin alamar karramawa da tunawa da marigayin, ina so in ayyana mako na zaman makoki daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Janairun 2024. A wannan lokaci na makoki, tutoci za su kasance a rabi.
"Ina umurtan daukacin al'umma da su yi anmfani da wadannan ranaku domin gudanar da addu’o’i sosai domin neman taimakon Allah Madaukakin Sarki wajen kare yankunanmu da kuma daura mu a kan mugayen mutanen da suka taso mana."
Ya ce abin farin ciki ne cewa duk da hare-haren da ake kai wa jama’a ba su karaya ba, ya kara da cewa kudurinsu na kare kasa da wadata ta na nan daram.
Mutfwang ya ci gaba da nuna kwarin gwiwa cewa shekarar 2024 za ta bayyana karfin zuciyar mutane da juriyarsu wajen fuskantar wadannan matsaloli.
Legit Hausa ta zanta da wata mazauniyar Filato, Larai Isah inda ta nuna bakin ciki kan kisan kiyashin da miyagu suka yi wa al’ummar jihar.
Larai ta yi kira ga gwamnatocin jihar da na tarayya a kan su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Larai ta ce:
“Muna yaba da kokarin gwamnati kan yadda ta nuna damuwa a irin kisan kare dangi da ake yi wa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba.
"Amma batun ware ranakun makoki ba shi bane, idan har gwamnati na son ta tabbatar mata tana tare da mu shine ta zakulo wadannan miyagu sannan a hukunta su tare da daukar matakan da za su hana sake faruwar irin haka a gaba, Muna rokon Allah ya kare wadanda suka rasa rayukansu sannan ya karemu mu da muka yi saura, domin dai kullun cikin fargaba muke har a cikin gida,”
Jerin yan siyasar da suka ziyarci Filato
A gefe guda, mun kawo a baya cewa hare-haren da yan bindiga suka kai kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi na jihar Filato a kwanan nan na ci gaba da haifar da martani daga yan Najeriya, kuma yan siyasa na ta zarya wajen don nuna tausayawarsu.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, a kalla gawarwaki 195 ne aka kirga zuwa yanzu na wadanda harin wanda ya faru a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba ya ritsa da su.
Asali: Legit.ng