“Ka Nemi Mata”: Martanin Jama’a Yayin da Dino Melaye Ya Koka da Rayuwar Kadaici, Bidiyon Ya Yadu

“Ka Nemi Mata”: Martanin Jama’a Yayin da Dino Melaye Ya Koka da Rayuwar Kadaici, Bidiyon Ya Yadu

  • Dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi na 2023, Dino Melaye, ya wallafa bidiyonsa yana girka abinci a turai
  • Dino Melaye, wanda ya kasance sanata a majalisar dokokin tarayya ta takwas, ya ce kowa ta kansa yake yi a turai, ba kamar Najeriya da yake da masu girka masa abinci ba
  • Wasu yan Najeriya da suka yi martani kan bidiyon, sun nemi a dubawa Sanatan mata don gudun cutar damuwa yayin da wasu suka bukace shi da ya yi aure don girki mai rai da lafiya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lokoja, Kogi - Sanata Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Kogi, ya yada wani bidiyonsa yana girka abinci a kicin, cewa "kowa ta kai a nan."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Abu 1 da Ba Zai Yi Tasiri ba a 2024

Melaye, wanda ya kasance sanata a majalisar dattawa ta takwas, ya ce idan da a Najeriya yake, da yana nan yana yi wa mai girka masa abinci ihun ya zama mai kazar-kazar a abun da yake yi.

An gano Dino yana girkawa kansa abinci
“Cutar Damuwa”: Martanin Jama’a Yayin da Dino Melaye Ya Koka da Rayuwar Kadaici, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Dino Melaye
Asali: Twitter

A cikin bidiyon, Melaye ya bayyana cewa da fari ya dafa wake kuma cewa ba da jimawa ba zai gayyaci makwabcinsa ya zo su shana tare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Abun da yan Najeriya ke fadi game da Dino Melaye da ke girki a kicin

Wasu yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na bidiyon don bayyana ra'ayoyinsu game da abun da tsohon sanatan ke yi. Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

Wata yar Najeriya a soshiyal midiya, @Nairaexchanger, ta bukaci a duba sanatan domin gujema cutar damuwa. Ta ce:

"Idan mutum ya kasance shi kadai a wannan shekarun, cutar damuwa na iya shigowa. Don Allah wani ya hada shi da budurwa yar Kogi mai kamun kai don ta daidaita hankalinsa.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

"A yi hakuri na karkatar da akalar tunani, don Allah wani ya hada shi da mai idon cin naira ta karbe dukkanin kudaden sata daga wajensa.

Wata mai amfani da dandalin mai suna, Esan Woman, ta ci gyaran tsohon dan majalisar kan yadda ya kamata ya yi girki yayin da ta bukace shi da ya je ya nemi mata. Ta rubuta:

"Oga Dino, don Allah ka wanke kayan lambunka kafin ka yanka ko kuma ka nemawa kanka matar aure."

Paul-Mark ya tambaya ko dai kudin biyan mai girki a can na da tayar da hankali ne idan aka mayar da shi naira. Ya rubuta:

"Kodai kudin biyan mai girki a can na da ban haushi ne idan aka mayar da shi naira,"

Matashi ya dinka tufafi da buhun Dangote

A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya wanda ya dade yana mafarkin gina gida ya sanya kaya na musamman da ya dinka da buhun simintin Dangote.

Shi da abokansa sun sanya tufafin yayin da yake magana kan burinsa na mallakar gida wata rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng