Rikici Ya Kunno Kai a APC Bayan Ganduje Ya Caccaki Jigon Jam’iyyar Kan Shugabanci, Bayanai Sun Fito

Rikici Ya Kunno Kai a APC Bayan Ganduje Ya Caccaki Jigon Jam’iyyar Kan Shugabanci, Bayanai Sun Fito

  • Dakta Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC ya caccaki jigon jam’iyyar, Salihu Lukman kan korafe-korafensa kan shugabancin jam’iyyar
  • Lukman wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ce a Arewa maso Yamma ya sha sukar tsare-tsaren jam’iyyar
  • Hadimin shugaban a bangaren wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinin 1 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullah Umar Ganduje ya soki jigon jam’iyyar a Najeriya, Salihu Lukman.

Lukman wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ce a Arewa maso Yamma ya sha sukar tsare-tsaren jam’iyyar.

Ganduje ya caccaki Salihu Lukman kan kalamnsa na batanci game da jam'iyyar
Ganduje Ya Caccaki Jigon Jam’iyyar, Lukman Kan Shugabanci. Hoto: Ganduje Umar, Salihu Lukman.
Asali: Facebook

Mene Ganduje ke cewa kan Lukman?

Kara karanta wannan

Ganduje ya yunƙuro, jam'iyyar APC ta fara shirin kwace mulki daga hannun wani gwamnan PDP

Ganduje ya bayyana Lukman a matsayin dan siyasa wanda ba shi da mafadi da kuma rashin sanin inda ya dosa, cewar New Telegraph.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin shugaban a bangaren wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinin 1 ga watan Janairu.

Okpala ya yi martani ne bayan Lukman ya kwatanta Ganduje da cewa ya na shugabanci irin na tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullah Adamu.

Ya kwatanta Lukman a matsayin wanda ba shi sakatar baki komai fada ya ke a tsawon shekaru.

Sanarwar ta ce:

“Kalaman da Lukman ya yi kan Ganduje ya tabbatar da cewa neman ta da zaune tsaye ya ke yi, ya na son bata sunan Ganduje da shugabancinsa.
“Mun san yadda Lukaman ya ke bakinsa babu sakata, dan jam’iyya ne da ke yakar kowa a jam’iyyar bai kamata a dauke shi da muhimmanci ba.

Kara karanta wannan

"Yadda Babangida da Obasanjo suka nemawa Buhari alfarmar takara a zaben Shugaban kasa"

“Ya kamata Lukman ya sani shugabancin APC na kan hanya kuma duk dan jam’iyyar ana tafiya da shi a harkokinta.”

Okpala ya ce Lukman ya zargi cewa APC ba ta gudanar da muhimman ganawa, shin dole ko wace ganawa sai an fada a gidan jaridu ko kafofin sadarwa?, cewar Daily Trust.

APC ta yi magana kan shari’ar Kano

A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana yadda ta ke da kwarin gwiwar samun nasara a shari’ar zaben Kano.

APC ta bayyana haka ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli bayan ta tanadi hukunci kan shari’ar zaben jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.