Yayin Da Ake Shan Daka a Najeriya, Buhari Ya Bayyana Dalilin Farin Ciki Da Ya Yi Bayan Cire Tallafi
- Yayin da ake fama da tsadar man fetur a Najeriya, tsohon shugaban kasa, Buhari ya ce haka dai-dai ne
- Buhari ya bayyana haka ne a birnin Katsina a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba yayin wani babban taro kan matasa
- Tsohon shugaban ya ce hakan ya yi masa dadi saboda yawan ziyara da mutane ke kai masa za ta ragu sosai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi.
Buhari ya ce kara kudin mai din ya rage yawan masu kai masa ziyara tun bayan barinsa kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Mene Buhari ya ce kan cire tallafin Tinubu?
Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba a birnin Katsina yayin wani taro da aka gudanar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya ce hakan ya masa dadi saboda masu yawan kai masa ziyara garin Daura da ke jihar Katsina tun bayan barinsa kujerar mulki za su ragu.
Ya kara da cewa cire tallafin mai din ya kara farashin mai din wanda ya ke tsammani zai rage baki zuwa gidansa da ke Daura.
Sai dai ya ce hakan bai rage komai ba ganin yadda suka nemo wata hanyar tara kudade don kai masa ziyarar, kasar yadda DCL Hausa ya yada bidiyon.
Buhari ya ce ya san wahalar Najeriya da dadinta
Ya ce:
"Wahalar Najeriya da dadinta na sani, alhamdulillahi na dawo gida na zauna mutane suna ta zuwa suna gaida ni a kullum.
"Da Tinubu ya kara kudin mai ina murna saboda baki za su ragu, amma sai su shirya su tara kudi su hau jirgi su fado min."
Idan ba a mantaba, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu yayin karbar rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa.
Tun bayan cire tallafin, 'yan kasar suka shiga wani mummunan yanayin wahalar rayuwa da tsadar kayayyakin masarufi, cewar Leadership.
Majalisa ta amince wa Tinubu karbar bashi
A wani labarin, Majalisar Dattawa ta sahalewa Shugaba Tinubu karbo basukan da ya bukata a kwanakin baya.
Tinubu ya bukaci amincewar Majalisar don karbar bashin dala biliyan 7.8 da kuma yuro miliyan 100.
Asali: Legit.ng