Shekarar 2023 Ta Zo Mana da Manyan Kalubale, Abba Kabir, Kwankwaso Sun Magantu Kan Shekarar 2024

Shekarar 2023 Ta Zo Mana da Manyan Kalubale, Abba Kabir, Kwankwaso Sun Magantu Kan Shekarar 2024

  • Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya taya al’ummar jihar Kano murnar shiga sabuwar shekarar 2024
  • Har ila yau, Sanata Rabiu Kwankwaso shi ma ya taya ‘yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar a yau Litinin
  • Wanna na kunshe ne a cikin sanarwa da suka wallafa a shafukansu na X a yau Litinin 1 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir da mai gidansa Rabiu Kwankwaso sun yi martani kan shiga sabuwar shekarar 2024.

Wanna na kunshe ne a cikin sanarwa da suka wallafa a shafukansu na X a yau Litinin 1 ga watan Janairu.

Kwankwaso, Abba Kabir sun magantu kan sabuwar shekarar 2024
Yayin da aka shiga sabuwar shekara, Kwankwaso, Abba Kabir sun yi jawabi. Hoto: Rabiu Kwankwaso, Abba Kabir.
Asali: Facebook

Mene Abba Kabir, Kwankwaso suka ce?

Kara karanta wannan

Dalilin daukar kudin kananan hukumomi 44 domin gina gadoji a birni Inji Abba Gida Gida

A martaninshi, Gwamna Abba Kabir ya taya dukkan jama’ar jihar Kano murnar shiga sabuwar shekarar lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya ce ya na da tabbacin cewa sabuwar shekarar da za a shiga za ta zamo shekarar samun ci gaba ga jihar Kano.

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin tabbatr da bukatun al’umma sun samu kulawa don samar da ci gaba a jihar.

Ya ce:

“Ina taya al’ummar jihar Kano murnar wannan rana, ina da tabbacin sabuwar shekarar za ta kawo ci gaban da ba a taba gani ba ga al’ummar jihar.
“Gwamnatina za ta ci gaba da kula da bukatun al’umma don samar da ci gaba a bangarori da dama a jihar.”

Wane addu'a suka yi?

Sanata Kwankwaso a bangarenshi ya bayyana jin dadinsa tare da gaisuwa ga ‘yan Najeriya kan bikin sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

2024: Kwanaki 2 da mutuwar gwamna, Lucky ya manta da shi ya ziyarci Tinubu kan wani babban dalili

Ya ce tabbas an samu matsaloli da dama a shekarar da ta gabata inda ya ce sabuwar shekarar za ta zo da ci gaba.

Ya ce:

“Ina cikin farin ciki da tura gaisuwa ga ‘yan Najeriya gida da waje kan murnar shiga sabuwar shekara.
“Tabbas shekarar da ta wuce an samu matsaloli a kasar baki daya, kuma ina fatan sabuwar shekarar za ta zo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Abba Kabir, Kwankwaso sun jajanta mutuwar Na’Abba

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano da Sanata Rabiu Kwankwaso sun nuna damuwa kan rasuwar Ghali Umar Na’Abba.

Sun bayyana hakan ne a shafinsu na X inda suka bayyana cewa tabbas jihar Kano da Najeriya sun yi babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.