Hotuna: 'Yan Hisbah sun kone kwallaben giya fiye da 300 a Katsina

Hotuna: 'Yan Hisbah sun kone kwallaben giya fiye da 300 a Katsina

- Kamar yadda ta ke faruwa a jihohi kamar Kano da Jigawa, Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta kama giya fiye da 300 a jihar

- Hukumar Hisbah ta kuma lalata giyan fiye da 300 da ke cikin kwallabe da gwangwani ta hanyar kona su

- A karkashin dokokin shari'ar addinin musulunci bai halasta ba musulmi su rika sha ko sayar da giya da sauran barasa

Hukumar Hisbah reshen Jihar Katsina da lalata giya fiye da 300 uku da ta kama cikin kwallabe da gwamgwanaye a sassan Jihar.

Ma'aikatan hukumar Hisban na karamar hukumar Daura ne suka gudanar da wannan aikin a ranar Talata 17 ga watan Nuwamban 2020.

DUBA WANNAN: Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

'Yan Hisbah sun kone kwalleben giya a Katsina
'Yan Hisbah sun kone kwalleben giya a Katsina. Hoto: Sani BelloBature
Asali: Facebook

An gano cewa giyan da suka lalata sun hada da Star da Life na cikin gwangwani da aka kwace daga hannun wasu dai-daikun mutane a karamar hukumar kamar yadda Sani Bello Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Jihar Katsina na cikin jihohin Najeriya da suka kadamar da aiki da shari'ar addinin musulunci wadda ta yi hani da sha da sayar da giya da sauran barasa a mafi yawancin sassan jihohin.

'Yan Hisbah sun kone kwalleben giya a Katsina
'Yan Hisbah sun kone kwalleben giya a Katsina. Hoto: Sani BelloBature
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal

'Yan Hisbah sun kone kwalleben giya a Katsina
'Yan Hisbah sun kone kwalleben giya a Katsina. Hoto: Sani BelloBature
Asali: Facebook

Wannan na zuwa ne kimanin kwanaki 10 bayan da Hisbah ta jihar Kano, ta fasa kwalaben giya 1,975,000 da kudinsu ya kai naira miliyan 200 a birnin Kano, Daily Trust ta wallafa hakan a ranar Lahadi.

Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna, yayin fasa kwalaben giyan a Kalebawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce shan giya zai iya janyo matsala ga kwakwalwar mutum, sannan Musulunci ya haramta.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon harajin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel