Kawun Gwamna Abba Kabir Na Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Gwamnan Ya Yi Martani
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga jimami bayan rasuwar kawunsa a yau Asabar 30 ga watan Disamba
- Marigayin Alhaji Hassan Yusuf Danmakwayi ya rasu ne a yau Asabar bayan ya sha fama jinya
- Sakon gwamnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Allah ya karbi rayuwar kawun Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a yau Asabar 30 ga watan Disamba.
Marigayin Alhaji Hassan Yusuf Danmakwayo ya rasu ne a yau Asabar bayan fama da jinya ya na da shekaru 72, cewar Daily Trust.
Mene Abba Kabir ya ce kan mutuwar?
Tuni aka binne shi kamar yadda tsarin addinin Musulunci ya tanadar a birnin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Sanusi ya ce marigayin wanda ma'akacin lafiya ne da ya yi ritaya ya rasu ya bar matarsa da 'ya'ya da dama da jikoki.
Danmakwayo shi ne kanin marigayi Alhaji Kabir Yusuf, mahaifi ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
M. Z Anka ya riga mu gidan gaskiya
Gwamnan ya yi addu'ar ubangiji ya masa rahama da ba shi gidan aljannar Firdausi mai daraja, SolaceBase ta tattaro.
Ya kuma yi addu'a ga iyalan mamacin da su jure hakurin rashin da suka yi na uba a danginsu.
Har ila yau, a jiya ne fitaccen dan siyasa Ambasada M.Z Anka ya riga mu gidan gaskiya a jihar Sokoto.
Marigayin wanda ya rasu bayan fama da jinya shi ne mahaifi ga kwamishinar lafiya, Dakta Aisha Anka a jihar Zamfara.
An yanke hukunci kan karar da aka shigar da Abba
A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta raba gardama kan shari'ar ciyamomin kananan hukumomi da kuma Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.
Kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano da kada ta taba kudaden ko kuma gudanar da wani aiki da kudaden na kananan hukumomin.
Wannan na zuwa ne bayan ciyamomin kananan hukumomin da kuma kungiyar ALGON sun maka gwamnan a kotu.
Asali: Legit.ng