Kano: Kotu Ta Raba Gardama Kan Karar da Ciyamomin Kananan Hukumomi 44 Suka Shigar da Abba Kabir

Kano: Kotu Ta Raba Gardama Kan Karar da Ciyamomin Kananan Hukumomi 44 Suka Shigar da Abba Kabir

  • Yayin da kananan hukumomin jihar Kano suka maka Gwamna Abba Kabir a kotu, an yanke hukunci kan matsalar
  • Kotun ta dakatar da Gwamna Abba Kabir kan amfani da kuma kashe kudaden kananan hukumomin
  • Kotun ta ce dole gwamnatin jihar ta dakatar da amfani da kudaden har sai bayan kammala shari’ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan amfani da kudaden kananan hukumomi a Kano.

Kotun ta dakatar da Gwamna Abba Kabir kan amfani da gudanarwa da kuma kashe kudaden kananan hukumomi 44, cewar Tribune.

Kotu ta raba gardama kan karar da aka shigar da Gwamna Abba Kabir
Kotu Ta Yi Hukuci Kan Karar da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Abba Kabir.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a shari'ar Kano?

Kara karanta wannan

An samu matsala bayan Hukumar Alhazai ta gaza cike yawan kujerunta dubu 95, an fadi babban dalili

Kotun ta ba da umarnin ne inda ta ce dole gwamnatin jihar ta dakatar da amfani da kudaden har sai bayan kammala shari’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari’a, D. U Okorowo shi ya ba da wannan umarni kan korafin da aka shigar a ranar 27 ga watan Disamba.

Har ila yau, kotun ta gargadi gwamnatin jihar kan taba kudaden dukkan kananan hukumomin guda 44, cewar Latest Nigerian News.

Wane umarni alkalin kotun ya bayar kan shari'ar?

Yayin hukuncin, alkalin kotun ya umarci wadanda ake kara da su halarci zaman kotun don ba da hujjar rashin dacewar dakatar da su kan haka.

Rahotanni sun tattaro cewa masu karar sun hada da dukkan kananan hukumomin jihar guda 44 da kungiyar ALGON reshen jihar.

Har ila yau, Gwamna Abba Kabir ya amince da biyan kudin diyyar rusau biliyan uku ga masu shaguna da 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Dalilin daukar kudin kananan hukumomi 44 domin gina gadoji a birni Inji Abba Gida Gida

Wannan na zuwa ne bayan kotun ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar guda 10 kan kudaden diyyar.

An maka Gwamna Abba Kabir a kotu

A wani labarin, Ciyamomin kananan hukumomi 44 sun maka gwamnatin jihar Kano a gaban babbar Kotun Tarayya.

Ciyamomin sun shigar da gwamnatin Abba Kabir a gaban kotun saboda yunkurin gina gadojin sama guda biyu.

Masu shigar da karar sun bukaci kotun ta bada umarnin hana gwamnatin Abba amfani da kudadensu na asusun hadin guiwa wajen gina gadojin saman guda biyu a cikin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.