Tashin Hankali Yayin da Dan Kasuwa Ya Nemi a Ba Shi Sojoji 16, Yan Sanda 20, DSS 12 Saboda Tsaro

Tashin Hankali Yayin da Dan Kasuwa Ya Nemi a Ba Shi Sojoji 16, Yan Sanda 20, DSS 12 Saboda Tsaro

  • Rashin tsaro a yankin kudu maso gabas ya sa shahararren dan kasuwar Anambra Nicholas Ukachukwu neman tsaro mai karfi
  • Ukachukwu ya bukaci a ba shi jami'an sojoji 16, yan sanda 20 da DSS 12 saboda tsaron kansa
  • Ya bukaci hakan ne bayan yan bindiga sun farmaki ayarin motocin jigon siyasar Anambra, Cif Chris Uba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Shahararren dan kasuwar Anambra, Nicholas Ukachukwu, ya bukaci a ba shi tsaro mai karfi bayan farmakin da yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Cif Chris Uba a jihar.

Ukachukwu ya bukaci a ba shi jami'an sojoji 16, yan sanda 20 da yan DSS 12 saboda tsaron kansa a wannan lokaci da ake ta shagulgula.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan gida daya su 8 sun mutu a hatsarin mota yayin zuwa bikin sabuwar shekara

Nicholas ya nemi a ba shi matakan tsaro
Tashin Hankali Yayin da Dan Kasuwa Ya Nemi a Ba Shi Sojoji 16, Yan Sanda 20, DSS 12 Saboda Tsaro Hoto: @ONsogbu
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, dan kasuwar ya yi bayanin cewa yana bukatar tsauraran matakan tsaro domin zuwa mahaifarsa, Osumenyi a karamar hukumar Nnewi ta kudancin jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan siyasar ya kara da cewar zai yi tafiya domin gudanar da wasu harkoki a farkon watan Janairun 2024.

Chris Uba ya tsallake rijiya a hannun yan bindiga

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki ayarin jagoran Peoples Democratic Party (PDP), Chris Uba, ranar Alhamis da daddare.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa maharan sun kai hari kan ayarin babban jigon PDP a kauyen Uga da ke ƙaramar hukumar Aguata a jihar Anambra.

Duk da ɗan siyasan ya tsallake rijiya da baya a motar sulƙen da yake ciki amma maharan sun yi nasarar bindige ƴan sanda biyu har lahira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa ayarin jagoran PDP wuta, sun tafka ta'adi tare da kashe rayuka

Yan bindiga sun kai farmaki Abuja

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan bindiga sun sake kai hari a ƙaramar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja.

Harin na zuwa ne bayan da ƴan bindiga suka mamaye ƙauyukan Tokulo da Garam da ke ƙaramar hukumar, inda suka harbe mutum uku tare da yin awon gaba da mutum shida.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a wani sabon harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Pandan-Gwari na ƙaramar hukumar, sun yi awon gaba da Hakimin ƙauyen da wasu mutum biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng