"Ina Neman Miji" Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Kuɗi Ta Fito Neman Wanda Zai Yi Wuff da Ita Ido Rufe
- Wata mata ta ja hankalin mutane a manhajar X yayin da ta wallafa wani saƙo daga wata budurwa mai neman mijin aure
- Sakon neman mijin ya kunshi abin da budurwar ta fi so da wurin zama tun daga Amurka zuwa Burtaniya, har da ƙabila
- Matar dai ta nemi duk wanda yake sha'awar ƴan matan ya tuntuɓe ta domin ta haɗa su da waɗanda ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wata kyakkyawar mace ƴar asalin Najeriya ta kudiri aniyar zama dillaliyar aure ta riƙa haɗa masu sha'awar aure da abokan rayuwa na har abada.
Matar mai suna @dearolaa ta wallafa kalolin masu neman aboka zama iri daban-daban da kuma wurare mabanbanta tun daga Amurka har zuwa Burtaniya.
Kai harma da ƙabilar da masu neman abokan zaman suka fito domin duk wanda ya gani yana so ya mata magana a haɗa su.
Matar ta wallafa sakon wata ƴar Amurka
Ɗaya daga cikin sakonnin neman mazan auren ya fito daga wata mace ƴar shekara 31 a duniya daga ƙasar Amurka, tana neman mijin aure na gaske ba zancen wasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya sa masu amfani da kafar sada zumuntan suka fara nuna sha'awarsu na neman abokan zama daga wasu ƙasashe, hakan ya kara ma labarin armashi.
Wani saƙon da ya ƙara jan hankali shi ne na wasu Musulmai maza guda biyu da ke neman a sama musu haɗi a ƙasar da suke rayuwa watau Burtaniya.
Olaa ta wallafa a shafinta cewa:
"Na faɗa muku shekarar nan ba zata fita kuna gwauraye ba, wannan kyakkyawar budurwar yar shekara 31 a ƙasar Amurka ta tura mun sakon neman mijin aure."
"Tana son mijin ya kasance ɗan Amurka ko Kanada. Wasu musulmai biyu da ke zama a Burtaniya suna son a sama musu haɗi a nan ƙasar. Haka wani kirista ya nemi a haɗa shi da wata a Burtaniya."
Martanin mutane kan bukatar ƴar Amurka
@LarryXcell ya ce:
"Tana son mijin ya zama ɗan ƙasar Amurka ko Kanada, lallai bata shirya aure ba."
@massive_Edafe ya ce:
"Watau dai ba ta bukatar ɗan Najeriya kenan."
@laurentdarl ya ce:
"Ni ma har yanzun gwauro ne."
@Dex2ro ya ce:
"Ko zan iya shiga cikin maneman ba'amurkiya yar shekara 31?"
Maganar aure ta fara rawa
A wani rahoton kuma Wani mutum ya nuna bacin ransa a soshiyal midiya bayan budurwarsa da ke farfadowa daga rashin lafiya ta bar gidansa cikin fushi
A cewar mutumin, budurwar wacce yake son aura ta harzuka saboda an ce ta dafa wa yan uwansa mutum 70 abinci.
Asali: Legit.ng