Gwamnatin Katsina ta dakatar da jami’i kan sayar da gandun daji
- An dakatar da Usman Illiyasu, shugaban sashin gandun daji a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina
- An dakatar da Illiyasu ne kan zargin samunsa da hannu a wajen sayar da gandun dajin Makaurachi
- Gwamnan Katsina, Dikko Radda ya kuma umurni hukumar yankin da ya gano duk wadanda ke da hannu a badakalar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta yi umurnin dakatar da Usman Illiyasu, shugaban sashin gandun daji a karamar hukumar Malumfashi, a ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba.
Gwamnatin ta dakatar da Illiyasu ne saboda zarginsa da hannu wajen siyar da wasu bangarori na gandun dajin Makaurachi da ke jihar, rahoton Punch.
Gwamnatin jihar ta ce sunan dakataccen shugaban sashin gandun dajin ya fito a cikin zargin sayar da wasu filaye ba bisa ka’ida ba, wanda ya kunshi dubban miliyoyin naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya fito ne a wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yada labarai, Alhaji Aliyu Yaradua, a madadin sakataren gwamnatin jihar, rahoton Channels TV.
Gwamna Dikko Radda ya kuma umurci hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi da ta zakulo duk jami’an da ke da hannu a cikin wannan badakala.
Sanarwar na cewa:
“Sunan Usman Illiyasu ya fito karara a cikin hada-hadar kudi da baya bisa ka'ida.
“Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya kuma umurci hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi da ta yi bincike sosai kan lamarin tare da tantance yadda ake hada-hadar kudi da baya bisa ka'ida kan filin.
“Gwamnan ya kuma ba da umarnin daukar matakin da ya dace kan wadanda aka samu da hannu a cikin badakalar”
An kuma umurci Hukumar yankin da ta "gaggauta" kai rahoto ga gwamnan.
Radda ya gwangwaje manoma a Katsina
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da shirin bunkasa noman rani kashi na farko ga manoma 2,040.
Wannan shiri dai na daga cikin yunkurinsa na bunkasa noma tare da inganta samar da abinci a fadin kananan hukumomin 34 na jihar.
Yayin kaddamar da shirin a Gwaigwaye da ke gundumar Dikke, karamar hukumar Funtua, gwamnan ya jaddada kudurin gwamnatinsa na bunkasa harkokin noma.
Asali: Legit.ng