Yan Gida Daya Su 8 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Zuwa Bikin Sabuwar Shekara

Yan Gida Daya Su 8 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Zuwa Bikin Sabuwar Shekara

  • Rundunar yan sandan jihar Imo ta tabbatar da mutuwar wasu yan gida daya su takwas a wani mummunan hatsarin mota
  • An rahoto cewa iyalin na a hanayrsu ta zuwa gida bikin sabuwar shekara ne lokacin da hatsarin ya afku
  • Hatsarin mai ban tsoro ya afku ne da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, a mararrabar Amanwozuzu da ke karamar hukumar Ikeduru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Imo - Wasu mutane takwas da ke hanyarsu ta koma gida domin bikin sabuwar shekara sun mutu a mummunan hatsarin mota a mararrabar Amanwozuzu da ke karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

Lamarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba, ya jefa al'ummar yankin cikin bakin ciki kasancewar mamatan duk yan gida daya ne, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Maganar aure na rawa bayan saurayi ya sa budurwa ta girkawa danginsa su 70 abinci, gishiri ya zarce

Hatsarin mota ya hallaka yan gida daya su 8
Yanzu-yanzu: Yan gida daya su takwas sun mutu a hatsarin mota Hoto: FRSC/The Nigerian Police
Asali: Facebook

Wasu da hatsarin ya afku a kan idanunsu sun bayyana cewa mahaifin iyalin wanda ke tuka mata da yaransa a cikin wata motar Sienna ya shigi wata babbar mota da ke fake dauke da karafuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hatsarin ya yi muni sosai domin dai karafunan sun tsire gawarwakin mutane da ke cikin motar kuma gaba dayansu suka mutu nan take.

A cewar wanda abun ya faru kan idonsa, jami'an yan sanda da al'ummar yankin sun fasa motar cikin hawaye domin fitar da gawawwakin iyalin.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, jami'an yan sanda daga karamar hukumar Ikeduru sun mika gawarwakin mamatan a dakin ajiyar gawa.

Rundunar yan sanda ta yi martani kan mummunan hatsarin da ya shafe iyali guda

DPO na yankin Ikeduru, Lucky Ahiole, ya fada ma manema labarai cewa an faka motar daukar kayan ne a gefen hanya lokacin da direban Siennan ya yi taho mugama da ita, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Ya ce:

“Abin akwai firgitarwa. Mutum takwas sun mutu kuma mun kai su dakin ajiye gawa. Dole muka fasa motar Sienna don fitar da gawawwakin. Karfe ya tsire idanuwansu da jikinsu hatta ga yaran sun mutu.”

Sai dai kuma, masu wucewa sun yi kira ga yan sanda a kan su bincike mamallaki ko direban motar da aka ajiye wanda ke dauke da karafuna don sanin dalilinda na toshe hanya.

Sun ce da a ce direban motar bai yi fakin a hanya ba, da za a iya dakile wannan bala'i.

An rasa rayuka a hatsarin mota

A wani labarin, mun ji cewa hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kaduna ta ce mutum huɗu sun mutu yayin da wasu 56 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamandan sashin, Mista Kabir Nadabo, ya bayyana cewa hatsarin motan ya auku ne a ƙauyen Sabon Sara da ke kan babbar hanyar a ranar Talata, cewar rahotoon Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng