“Akwai Aiki Babba Gabanka”: Abin da Shugaba Tinubu Ya Fadi Wa Sabon Gwamnan Ondo, Aiyedatiwa
- Sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a birnin Legas, inda suka tattauna muhimman abubuwa
- Jim kadan bayan kammala ganawar, Gwamna Aiyedatiwa ya ce ya ziyarci shugaban kasar don sanar da shi abubuwan da suka faru a jihar
- A ziyarar, shugban kasa Tinubu ya ba Aiyedatiwa shawarwari na yadda zai gudanar da shugabanci a jiharsa, bayan mutuwar Akeredolu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Legas - A ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, Shugaba Bola Tinubu ya gana da sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a jihar Legas, inda ya ba shi wasu shawarwari.
Jim kadan bayan ganawar, Gwamna Aiyedatiwa ya zanta da manema labarai, inda ya ce ya je ne domin ba shi rahoton abubuwan da suka faru a jiharsa ta Ondo.
Abin da Tinubu ya fadi mun - Aiyedatiwa
A ranar Laraba ne aka rantsar da Gwamna Aiyedatiwa matsayin gwamnan Anambra biyo bayan mutuwar Gwamna jihar Rotimi Akeredolu a ranar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko da aka tambaye sa abin da Shugaba Tinubu ya fada masa yayin ganawar, The Nation ta ruwaito Aiyedatiwa na cewa:
"Shugaba Tinubu ya yi mana ta'aziyyar rasuwar gwamnan jihar mu, ya kuma yi mun fatan alkairi tare da kara karfafa mun guiwa don fuskantar babban aikin da ke gabana.
"Ya kuma bani tabbacin goyon bayansa, inda ya yi nuni da yadda Allah ke canja lamuransa ta fuskar hawa da sauka kujerar mulki, kamar yadda na hau mulkin yanzu."
Dalilin da ya sa Aiyedatiwa ya kai wa Tinubu Ziyara
Da ya ke fadin dalilin ziyartar shugaban kasar da ya yi, Aiyedatiwa ya ce:
"Na gana da shugaban kasar don sanar da shi abubuwan da suka faru a jihar; mutuwar gwamna Akeredolu da kuma rantsar da ni matsayin sabon gwamna.
"Na kuma yi masa godiya kan dattakun da ya nuna a watanni shida da suka wuce na rikicin siyasar da ya mamaye Anambra, ya tsaya mana har komai ya zama tarihi."
A wani bangaren, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda shi ma ya ziyarci shugaban kasar a ranar Alhamis ya jajanta masa da kuma ba shi ba'asin abinda ya faru a jiharsa.
Kwamishinan jihar Ondo ya yi murabus, ya fadi dalili
Kasa da awanni 24 bayan rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, kwamishinan gine-gine, filaye da gidaje na jihar Raimi Aminu ya yi murabus.
Mr Aminu ya ce babu dalilin ci gaba da rike mukamin alhalin uban gidansa a siyasa kuma wanda ya bashi mukamin Rotimi Akeredolu ya rasu, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng