Kano: Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Shugaban Karamar Hukuma, Ta Yi Hukunci Mai Tsauri
- Dakataccen shugaban karamar Gwale ya sake samun cikas bayan kotu ta yi hukunci kan matsalar
- Babbar Kotun jihar Kano ta umarci shugaban karamar hukumar, Khalid Ishaq Diso daga alakanta kansa a matsayin shugaban rikon karamar hukumar
- Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar jihar ta dakatar da Diso kan wasu zarge-zarge da badakala a ofishinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babbar Kotun jihar Kano ta yi hukunci kan sahihancin kasancewar Hon. Ishaq Khalid Diso a matsayin shugaban rikon karamar hukumar Gwale.
Kotun ta dakatar da Diso kan ci gaba da kiran kansa a matsayin shugaban rikon karamar hukumar da ke Kano.
Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?
Har ila yau, kotun ta umarci Diso da sauran mukarrabansa da su guji aiwatar da wani aiki a karamar hukumar har zuwa lokacin karkare shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar jihar ta dakatar da Diso kan wasu zarge-zarge da badakala a ofishinsa, Leadership ta tattaro.
An kara tsawaita dakatarwar da aka yi wa shugaban karamar hukumar har zuwa ranar 30 ga watan Janairun 2024.
Yaushe za a ci gaba da sauraran karar a Kano?
Masu shigar da karar, Ghali Nalele Bature da Ghali Umar Diso su na kalubalantar shugaban karamar hukumar da ma'aikatar kananan hukumomi da Majalisar jihar.
Sauran wadanda ake karar sun hada da karamar hukumar Gwale da kuma kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, cewar AllNews.
Za a ci gaba da shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Janairun 2024 inda ake tsammanin wasu sabbin korafe-korafe kan Diso da matsalar shugabanci.
Abba Kabir ya amince da biyan diyyar rusau
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya amince da biyan kudaden diyya ga wadanda matsalar rusau ta shafa a jihar.
Abba ya amince da biyan naira biliyan uku bayan masu shaguna da kungiyar 'yan kasuwa sun maka shu a kotu kan asarar da suka tafka.
A baya kotu ta umarci gwamnan da ya biya naira biliyan 30 wanda ya jawo rufe asusun bankunan gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng