Kano: An Tsare Matashi a Gidan Kaso Kan Barazanar Kawo Karshen Dattawan Unguwarsu, Ya Fadi Dalili

Kano: An Tsare Matashi a Gidan Kaso Kan Barazanar Kawo Karshen Dattawan Unguwarsu, Ya Fadi Dalili

  • An cafke wani matashi kan zargin yi wa dattawan Unguwarsu barazanar hallaka su gaba daya a jihar Kano
  • Kotun Majistare ta umarci tsare matashin inda ya tabbatar da furta kalaman yi musu barazana kan wata matsala
  • Wanda ake zargin mai suna Musa Okashatu Gobirawa da barazanar hallaka wasu dattawa a Unguwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Kotun shari’ar Musulunci da ke jihar Kano ta umarci tsare wani matashin kan zargin karar da dattawan Unguwarsu.

Wanda ake zargin mai suna Musa Okashatu Gobirawa ya yi barazanar hallaka wasu dattawa a Unguwarsu da ya ke zargin za su kwace filinsa.

Kotu ta tsare matashi a Kano kan zargin arar da dattawan Unguwansu
Ana zargin matashin ne da barazana ga dattawan Unguwansu. Hoto: @KanoPoliceNG.
Asali: Facebook

Wane mataki kotun ta dauka kan matashin a Kano?

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta dauki mataki kan shari'ar Hafsat 'Chuchu' da ake zargi da kisan kai, ta yi bayani

Kotun ta umarci tsare shi a gidan kaso inda ta ce aikata hakan ya sabawa sashi na 227 na kundin laifuka da hukuncin Shari’ar Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama wanda ake zargin ne bayan wasu Muhammad Sani Hussain da Bashir Namoriki sun shigar da kara gaban kotun, cewar Daily Trust.

Wanda ake zargin ya yi barazanar ce bayan mambobin kwamitin Unguwar sun yi zama inda suka kawo wata doka wacce ba ta masa dadi ba.

Mene martanin matashin da ake zargin a Kano?

Har ila yau, wanda ake zargin ya amince da furta kalaman yayin da mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa laifukan.

Ya ce ya fusata ne bayan mambobin kwamitin sun yi kokarin kwace masa filinsa inda suka ce ba na shi ba ne, cewar Tori News.

Mai Shari’a, Mallam Nura Yusuf ya umarci tsare matashin tare da dage sauraran karar zuwa ranar 11 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Kotu ta yi hukunci kan shari’ar Hafsat ‘Chuchu’ a Kano

A wani labarin, Kotun Majistare ta umarci ci gaba da tsare Hafsat Surajo da ake zargi da kisan kai a Kano.

Ana zargin Hafsat da zargin hallaka abokin kasuwancinta mai suna Nafi’u Hafizu bayan sun samu hatsaniya a tsakaninsu.

Kotun daga bisani da dage ci gaba da sauraran shari’ar har sai ranar 1 ga watan Faburairun 2024 da za mu shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.