Tashin Hankali Yayin da Jami'in Dan Sanda Ya Rasa Ransa a Hannun Budurwarsa, An Fadi Abin da Ya Faru

Tashin Hankali Yayin da Jami'in Dan Sanda Ya Rasa Ransa a Hannun Budurwarsa, An Fadi Abin da Ya Faru

  • Wani jami'in ɗan sanda mai suna Cosmos Ugwu ya rasa ransa bayan budurwarsa ta harbe shi a yankin Ezinihitte dake jihar Imo
  • Ugwu ya rasa ransa ne bayan budurwarsa ƴar shekara 23 ta harbe shi da bindigarsa a lokacin da suka fafata da juna a ranar Talata, 26 ga watan Disamba
  • Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya bayyana cewa ana shirin gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ezinihitte, jihar Imo - Amanda Uchechi Ugo ƴar shekara 23 ta shiga hannun jami'an tsaro bisa harbe wani saurayinta ɗan sanda mai suna Cosmas Ugwu har lahira a jihar Imo.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Talata, 26 ga watan Disamba, a ofishin ƴan sanda na yankin Ezinihitte.

Kara karanta wannan

Babban basarake ya kubuta daga hannun yan bindiga bayan an biya N6m da wasu abubuwan ban mamaki

An halaka dan sanda a Imo
Budurwa ta bindige saurayinta dan sanda a Imo Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wata majiya ta ce likita ne ya tabbatar da rasuwar marigayin bayan an garzaya da shi asibitin Evergreen da ke Ezinihitte nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Amanda ta harbe shi har sau uku a ƙirjinsa da kuma hannun hagu ta hanyar yin amfani da bindigarsa a yayin da suke fafata rikici.

Wata majiya ta bayyana cewa:

"A zahiri babu wanda ya san abin da ya faru tsakanin su biyun, amma yadda yarinyar ta yi amfani da bindigar ƴan sanda cikin nasara har yanzu abin mamaki ne ga mutane da yawa. Wataƙila Ugwu ne ya koya mata."

Ƴan sandan Imo sun mayar da martani

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da jaridar The Nation ta wayar tarho.

"Eh, lamarin ya faru. Wani jami'in ɗan sanda ya rasa ransa bayan budurwarsa ta harbe shi har lahira. Yana aiki a Ezinihitte Mbaise."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari ana shirin taron addini a arewa, sun kashe sama da 15

"A yanzu haka an kama budurwar, muna yin duk mai yiwuwa domin ganin mun gudanar da bincike a kan lamarin, gano gaskiyar lamarin, da kuma yiwuwar gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu."

Budurwa Ta Halaka Saurayinta a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata budurwa ta yi ajalin saurayinta har lahira bayan ta ɗaba masa wuƙa a jihaɗ Rivers.

Budurwar dai ta aikata wannan ɗanyen aikin ne bayan wata ƴar hatsaniya ta ɓarke a tsakaninta da saurayin na ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng