“Ban Yi Danasani Ba”: Budurwa Ta Kashe Miliyan 1.9 Kan Turaruka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

“Ban Yi Danasani Ba”: Budurwa Ta Kashe Miliyan 1.9 Kan Turaruka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wata matashiya ta bayyana yadda ta yi siyayya tare da kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 1.9 a kan turaruka
  • Duk da wannan almubazzaranci da ta yi, ba ta nuna nadama ba kuma ta yarda cewa ita ma'abociyar son kamshi ce
  • Wannan ya haifar da cece-kuce daga jama'a da suka cika sashin sharhinta domin bayyana ra'ayoyinsu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wata wallafa da ta yi a TikTok, wata matashiya ta ba da labarin kasaitaccen siyayya da suka je ita da kawarta suka yi.

Yan matan biyu sun kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 1.9, tama mai cewa suna matukar son kamshi.

Budurwa ta kashe makudan kudade kan turare
“Ban Yi Danasani Ba”: Budurwa Ta Kashe Miliyan 1.9 Kan Turaruka, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @rachaelscloset/TikTok
Asali: TikTok

Matashiya ta yi suna bayan ta siya turarukan 1.9

Kara karanta wannan

Wata attajirar mata ta gwangwaje yan biki da tukunyar gas, bidiyon ya girgiza intanet

Duk da makudan kudaden da suka kashe, matar mai suna @rachaelscloset_ ta tsaya tsayin daka kan shawarar da ta yanke kuma ba ta nuna nadama ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka tambayeta ko ta nadamar makudan kudaden da suka kashe kan haka, cike da kwarin gwiwa matashiyar ta ce bata yi ba.

Halin ko'inkula da ta nuna kan almubazarancin da ta yi ya nuna tsantsar sonta ga turaruka, inda ta bayyana cewa wanka ya biya kudin sabulu.

Ta ce:

"Shin na yi danasani? A'a. Za sake aikata haka? Eh! Kun ga ina matukar son Turaruka."

Martani yayin da budurwa ta kashe miliyan 1.9 kan turaruka

Bidiyon matashiyar ya dauka hankali sosai inda mutane suka gaggauta yin martani a kan tsadadden siyayya da ta yi.

Shezprecious2001 ta ce:

"Wayyo Allah a ina irin wadannan kwastamomin suke ne."

Kara karanta wannan

Ba Dani Ba: Sheikh Dahiru ya yi martani kan wasikar da aka ce ya rubuta kan rikicin Abba da Gawuna

TYRAN ta yi martani:

"Ina so na zama kamar ke idan na girma."

Debbie ta yi martani:

"Yan matan 1.9m."

Matar gwamna ta girgiza intanet da kyauta

A wani labarin, an ga bidiyo mai tsuma zuciya na wata mata da ta kashe miliyoyin kudi don siyawa mijinta kyaututtuka na bazata ya ja hankalin TikTok.

Bidiyon, wanda aka yada a TikTok, ya nuna matar wacce ke cike da farin ciki yayin da ta nunawa duniya kayayyaki iri-iri da ta siyawa mijinta, wanda sam baya sane da shirinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng