Yadda wani mutum ya damfari dan sanda da wasu mutum 14

Yadda wani mutum ya damfari dan sanda da wasu mutum 14

Wani mutum mai suna Labaran Aliyu mai shekaru 33 a yankin Gidan Buhari da ke karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto, ya shiga hannun hukuma a kan zarginsa da ake yi da damfarar wasu mutum 15 da suka hada da dan sanda.

Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Sokoto, Dr. Adamu Bello Kasarawa, ya zargi wanda ake zargin da karbar kudi har naira miliyan 2.4 daga wurin wadanda ya damfarar da sunan zai buga musu kudi.

Kamar yadda hukumar Hisbah ta bayyana, wadanda ya damfarar ''yan jihohi daban-daban ne na sassan kasar nan.

"An kama wanda ake zargin bayan korafinsu sannan kuma an samu lambobin wayarsu a cikin wayar salularsa".

Ya ce dan sandan da aka damfara, amma an boye sunansa, a halin yanzu yana aikinsa a jihar Kaduna.

"Yana amfani da sihiri, yankan dabbobi, aljanu da duk wasu nau'in turaruka wurin yaudarar jama'a da damfara," Karasawa yace.

Abubuwan da aka samu daga hannun dan damfarar sun hada da dalolin Amurka na bogi da kuma kudaden gida Najeriya daban-daban.

Kwamandan ya kara da bayyana cewa, ana zargin mutumin da lalata wasu kananan yara uku a lokuta daban-daban sannan ya nadi lamarin a wayarsa.

"Ya nadi yadda yake lalata da wasu kananan yara a wayarsa wacce a halin yanzu take wurin 'yan sandan," kwamandan ya zarga.

Kasarawa ya ce an mika wanda ake zargin hannun 'yan sanda domin su karasa bincike tare da mika shi wurin ladabtarwa.

Yadda wani mutum ya damfari dan sanda da wasu mutum 14
Yadda wani mutum ya damfari dan sanda da wasu mutum 14. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Damfara: EFCC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram tare da wasu mutum 4

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai farmaki a kasuwar Kusasu da ke cikin karamar hukumar Shiroro, jihar Niger kuma sun yi awon gaba da mutane tara. Lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga kasuwar ne domin diban kayan abinci da sauran kayan bukatun su, inda suka kare da yin garkuwa da mutane tara.

Wakilin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun shiga kasuwar ne da tsakiyar rana, haye a saman babura sama da 15, kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Yan bindigar a cewar wata majiya mai tushe, sun tuntubi iyalan wadanda suka yi garkuwa da su bayan kwanaki uku, sun bukaci N10m a matsayin kudin fansar mutanen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel