Farashin Mai Zai Zube Gaba Daya, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Shekarar 2024, Ya Fadi Sauran Abubuwa

Farashin Mai Zai Zube Gaba Daya, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Shekarar 2024, Ya Fadi Sauran Abubuwa

  • Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara, Fitaccen Fasto ya yi hasashe masu muhimmanci kan shekarar
  • Fasto Philip Goodman ya ce Kiristoci su shirya tarbar Yesu Almasihu saboda ya hango ya kusa zuwa gare su
  • Fasto Goodman ya ce za a samu karyewar farashin danyen mai wanda hakan dole zai saukar da farashin man fetur

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Fitaccen Fasto a Najeriya, Philip Goodman ya yi hasashen shekarar 2024 za a yi ta cikin nasara.

Fasto Goodman ya ce za a samu karyewar farashin danyen mai wanda hakan dole zai saukar da farashin man fetur a kasar.

Jerin hasashen da malamin addini ya yi kan shekarar 2024
Fasto Philip Goodman ya yi hasashen abubuwan da za su faru a 2024. Hoto: Goodman A. Philip.
Asali: Facebook

Mene Faston ya ce kan shekarar 2024?

Kara karanta wannan

Bankin Duniya ya lissafo jihohin da talauci, wahala da rashin tsaro za su karu a 2024

Faston ya bayyana haka ne a sanannen shafinsa na Facebook a jiya Laraba 27 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shekarar 2024 za ta zo da abun mamaki inda ya ce hukuncin Ubangiji zai tabbata kan shugabanni masu cin hanci.

Wannan hasashen Faston na zuwa ne yayin da al'ummar Kirista a fadin duniya ke bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

Ya ce:

"Hasashen annabta na shekarar 2024.
"Amos 3:7 tabbas Ubangiji ba zai yi wani abu ba amma ya na bayyana sirrikansa ga bayinsa."

Jerin hasashen da Faston ya yi

1. 2024 shekara ce da masu bi za su yi nasara.

2. Shekarar 2024 duk da dala za ta yi mummunan tashi amma masu bi za su yi rayuwa da imaninsu.

3. A 2024 danyen mai zai karye wanda hakan zai yi sanadin karyewar farashin man fetur a kasar.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 5 muhimmai da ya kamata Ku sani game da marigayi Ghali Umar Na'Abba

4. Shekarar 2024 zai bai wa na karshe damar dawo wa farko yayin da na farko zai koma karshe.

5. Har ila yau, a shekarar 2024 na hango mataimakin gwamnan jihar Edo zai kasance gwamna.

6. Na hango zuwan Yesu Almasihu don haka Kiristoci su shirya kasancewa da shi.

Fasto ya gargadi 'yan uwansa kan rikincin Isra'ila

A wani labarin, Fitaccen Fasto a Najeriya, Chukwuemeka Odumeji ya gargadi 'yan uwansa Fastoci kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

Faston ya yi barazanar makantar da su idan har ba su bar taya Isra'ila addu'o'i ba yayin da ake ci gaba da gwabza yaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.