Akwai Matsala: An Bankado Shirin Kawo Hargitsi a Arewacin Najeriya

Akwai Matsala: An Bankado Shirin Kawo Hargitsi a Arewacin Najeriya

  • Wasu ƙungiyoyin cigaban yankin Arewacin Najeriya sun bankaɗo shirin da ake yi domin kawo hargitsi a yankin
  • Ƙungiyoyin AYCF da NEN sun bayyana cewa sun gano ana shirin ɗaukar nauyin gudanar da zanga-zanga a yankin domin kawo hargitsi
  • Ƙungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya idanu sosai domin kawar da mummunan shirin da ake ƙullawa kan yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙungiyar tuntuɓa ta matasan Arewa (AYCF) da kuma Northern Emancipation Network (NEN) sun bankaɗo shirin haifar da rashin zaman lafiya a yankin Arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƙungiyoyin sun bayyana cewa ana son ayi amfani da jihar Zamfara a matsayin cibiyar gudanar da wannan mummunan shirin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Sabuwar rigima ta barke tsakanin APC da gwamnatin Kano kan abu 1

AYCF ta bankado shirin kawo hargitsi a Arewa
Kungiyoyin AYCF da NEN sun bankado shirin kawo hargitsi a Arewacin Najeriya Hoto: @yerima_shettima
Asali: Instagram

AYCF ta yi kira ga gwamnatin tarayya

Domin haka ƙungiyoyin suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki tsatsauran mataki kan duk wani mai tayar da hankali da aka samu a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin sun kuma yi kira ga alƙalan kotun ƙoli da su yi nazari sosai kan hujjojin da ke gabansu yayin yanke hukunci, rahoton Trust Radio ya tabbatar.

Shugaban ƙungiyar AYCF, Yerima Shettima, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa suna da sahihin bayanai dangane da aniyar wasu mutane na ɗaukar nauyin gudanar da zanga-zanga a faɗin yankin Arewa domin cimma muradunsu na ƙashin kai.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Domin haka ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya musamman hukumar ƴan sandan fararen kaya (DSS) da ta sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa."
"Muna gargaɗin al’ummar Zamfara da su kasance cikin shiri, su bijirewa duk wani yunƙuri na tunzura su da aikata miyagun ayyuka."

Kara karanta wannan

Ana dab da yanke hukunci, jam'iyyar APC ta bankado sabuwar kulla-kullar da gwamnatin Kano take yi

Jam'iyyar APC ta bankaɗo shirin gwamnatin Kano

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kano, ta bankaɗo shirin gwamnatin jihar na yin sama da faɗi da Naira biliyan takwas.

Jam'iyyar ta bayyana cewa gwamnatin na shirin wawushe kuɗin ne daga asusun jihar domin rashin tabbas kan yadda shari'ar zaɓen gwamnan jihar za ta kaya a kotun ƙoli.

Shari'ar Zaɓen Nasarawa Ta Bar Baya da Ƙura

A baya kun ji cewa wasu ƙungiyoyin mata na cigaba da gudanar da zanga-zanga kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa, wacce yanzu haka ke a gaban kotun ƙolin ƙasar nan.

Matan dai suna yin zanga-zanga kan abin da suka kira rashin adalcin da aka yi musu a kotun ɗaukaka ƙara, bayan kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng