Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Dira a Jihar Arewa Bayan Kashe Bayin Allah Sama da 100

Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Dira a Jihar Arewa Bayan Kashe Bayin Allah Sama da 100

  • Sanata Kashim Shettima ya ziyarci jihar Filato domin duba waɗanda hare-haren jajibirin kirsimeti ya shafa a kananan hukumomi 2
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya samu tarba daga NSA, babban hafsan tsaro, Gwamna da wasu jiga-jigai a jihar
  • Wannam ziyara na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kisan da wasu yan ta'adda suka yi wa bayin Allah sama da 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Jihar Plateau - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya dira a Jos, babban birnin jihar Filato domin ziyartar waɗanda hare-haren jajibirin kirsimeti ya shafa.

A rahoton Channels tv, Shettima ya ziyarci ƴan gudun hijarar da suka baro gidajensu sakamakon harin wasu miyagu ana gobe bikin kirsimeti a ƙaramar hukumar Bokkos.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dau zafi kan harin Plateau, ya ba jami'an tsaro sabon umarni

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Yanzun nan: Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Dira a Jihar Arewa Bayan Kashe Bayin Allah Sama da 100 Hoto: The Time Is Now/Fb
Asali: Facebook

Jirgin da ya ɗauko mataimakin shugaban kasar ya taɓa ƙasa ne da misalin karfe 1:00 na rana yau Laraba a filin sauka da tashin jiragen sama na Yakubu Gowon da ke Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya kai wannan ziyara ne domin duba ƙauyuka sama da 20, wanda makasan suka kai farmakin rashin imani a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi.

Jiga-jigan da suke je tarban Shettima a filin jirgi

Mataimakin shugaban ƙasar ya samu tarba mai kyau daga mai bada shawara kan tsaro, Nuhu Ribado, babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, da Gwamna Celeb Mutfwang.

Tsoffin gwamnonin jihar Filato guda biyu, Sanata Simon Bako Lalong da Joshua Dariye na cikin tawagar da suka tarbi Sanata Shettima.

Tuni dai ‘yan gudun hijirar suka hallara a karamin filin wasa na karamar hukumar Bokkos, suna jiran ƙarisowar mataimakin shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje

Yadda mummunan lamarin ya faru

Galibi mata da kananan yara, ‘yan gudun hijirar sun ba da labarin yadda ‘yan bindiga suka kai musu hari inda suka kona gidajensu tare da kashe ‘yan uwansu sama da 100.

Harin wanda ya auku a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi ranar jajibirin kirsimeti, ya bar wasu mutane akalla 300 kwance a asibiti.

An ga wadanda abin ya shafa dauke da alluna masu rubuce-rubuce irin su ‘Dole a Kare Hakkinmu Na Dan Adam’, da dai sauransu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

CBN ya musanta shirin kwace wasu bankuna

A wani rahoton na daban Babban bankin Najeriya CBN ya musanta cewa FG zata kwace wasu bankuna kuma duk wanda ya ajiye kuɗi ya yi asara.

A wata sanarwa da CBN ya fitar ya tabbatarwa duk wani mai ajiya a bankunan Najeriya cewa kudinsa na cikin aminci da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262