Ganduje Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Mai Ratsa Zuciya Kan Rasuwar Ghali Na'Abba

Ganduje Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Mai Ratsa Zuciya Kan Rasuwar Ghali Na'Abba

  • A safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba aka tashi da labarin rasuwar tsohon kakakin majalisar wakilai
  • Marigayi Ghali Umar Na'abba ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi jinya kan lalurar da ba a bayyana ba
  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya aike da saƙon ta'aziyyar marigayin inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen mutum mai kishin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja- Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Dr Abdullahi Ganduje ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon kakakin majalisar wakilai, marigayi Ghali Umar Na’Abba.

Marigayi Ghali Umar Na'Abba mai shekara 65 a duniya, ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja a safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Na'Abba: Kwankwaso, Abba Kabir sun kadu kan rasuwar tsohon kakakin Majalisa, sun tura muhimmin sako

Ganduje ya yi ta'aziyyar Ghali Na'abba
Ganduje ya yi Addu'ar Allah ya jikan Ghali Na'abba Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Kano Online
Asali: Facebook

A cewar majiyoyi daga iyalan marigayin, ya daɗe yana fama da ciwon da ba a bayyana ba kafin rasuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta ce Ganduje, a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran sa, Edwin Olofu, ya rabawa manema labarai, ya bayyana Na’Abba a matsayin gogaggen ɗan siyasa kuma ɗan majalisa wanda ke da kyakkyawar niyya ga ƙasar nan.

Ganduje ya bayyana rawar da Ghali Na'Abba ya taka

Ya yi nuni da gagarumar rawar da tsohon jigon na jam’iyyar adawa ta PDP ya taka a lokacin da ya riƙe muƙamin shugaban majalisar wakilai wajen tabbatar da ƴancin cin gashin kan ƴan majalisar, duk da ƙalubale daga ɓangaren zartaswa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ƙwarewarsa da jajircewarsa ko da aka yi masa barazanar tsigewa sun taimaka wajen duk irin nasarar da aka samu a majalisar tarayya a yau. Ya yi wa Najeriya hidima. Basirarsa, hikimarsa da halayyyarsa abun a yaba ne."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi ta'aziyyar Ghali Na'abba, ya bayyana muhimmin abu 1 da ya yi domin ceto Najeriya

Ganduje ya yi addu'ar Allah ya ba shi Aljannah Firdaus, ya kuma ba iyalansa da sauran al’ummar jihar Kano da ƴan Najeriya baki ɗaya haƙurin rashinsa.

Shehu Sani Ya Yi Ta'aziyyar Ghali Na'Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya aike da ta'aziyyya kan rasuwar Ghali Umar Na'Abba.

Tsohon sanatan ya bayyana rasuwar tsohon kakakin majalisar a matsayin babban rashi ga iyalansa da ƙasa baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng