Abun Bakin Ciki Yayin da Matar Tsohon Shugaban PDP da Surukarsa Suka Mutu a Jajiberin Kirsimeti
- Mazauna karamar hukumar Ukanafun a jihar Akwa Ibom, sun shiga juyayi yayin da gobara ta lalata dukiya da iyalin tsohon shugaban PDP, Obong Udo Ekpenyong
- Har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, amma jam’iyyar PDP reshen jihar ta shiga firgici da alhini
- Sakataren kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Udeme Idiong ya fitar da wata sanarwa inda ya tabbatar da aukuwar lamarin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Akwa Ibom, Uyo - A wani lamari mai karya zuciya, gobara ta lakume gidan marigayi shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Akwa Ibom, Obong Udo Ekpenyong.
Yadda gobara ta halaka matar tsohon shugaban PDP da surukarsa
Lamarin wanda ya afku a jajiberin ranar Kirsimeti a karamar hukumar Ukanafun da ke jihar a ranar Lahadi, 24 ga watan Disamba, ya kuma yi ajalin matar marigayin, Misis Elizabeth Udo Ekpenyong, da kanwarta, Ofonime Frank.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, har yanzu ba a san dalilin faruwar gobarar wanda ya jefa al'umman Ukanafun cikin bakin ciki.
Sakataren kwamitin riko na karamar hukumar, Udeme Idiong, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 27 ga watan Disamba.
Da yake martani, shugaban riko na karamar hukumar Godwin Ekpe, ya ayyana kwanaki bakwai na zaman makoki ga al'ummar yankin.
"Muna addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu yayin da muke jajantawa iyalan mamatan."
Gobara ta lakume shaguna 30
A wani labarin kuma, mummunar gobara ta lakume shaguna akalla 30 a babbar kasuwar Nkpor da ke jihar Anambra.
Lamarin ya faru a yau Laraba 20 ga watan Disamba inda aka tafka mummunan asara a kasuwar da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa.
Gobara ta tashi gidan tsohon gwamna
A gefe guda, mun kawo cewa akalla mutum biyu suka mutu a wata gobara da ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala.
Kwamandan hukumar kashe gobara na Obomoso, Mr Oluwaseyi Awogbile, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda gobarar ta fara karfe 7:30 na safiyar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023.
Asali: Legit.ng