Tsohon Gwamnan CBN Ya Ƙara Bankado Muhimmin Abu Kan Emefiele a Mulkin Buhari da Jonathan
- Tsohon gwamnan babban banki, Kingsley Moghalu, ya ayyana Godwin Emefiele a matsayin mafi munin gwamnan CBN a tarihin Najeriya
- A wani sako da ya wallafa a shafinsa ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, Moghalu ya feɗe lokacin Emefiele a CBN
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya zargi tsoffin shugabanni biyu, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari bisa aminta da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Kingsley Moghalu, ya yi magana kan wa'adin da Godwin Emefiele ya shafe a matsayin gwamnan CBN.
Moghalu ya bayyana cewa, "babu tantama Emefiele shi ne gwamnan CBN mafi muni da cutarwa da aka taɓa yi a tarihin Najeriya."
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Moghalu ya ce tsohon gwamnan CBN ɗin, "bai cancanta ba kuma bai shirya riƙe muƙamin ba ko kaɗan."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Emefiele ya lalata komai a matsayin gwamnan CBN
Farfesan ya kuma bayyana cewa "daga dukkan bayanan da suka fito a yanzu," Emefiele ba shi da gaskiya.
Tsohon shugaban ƙasa, Dokta Goodluck Jonathan ne ya naɗa Emefiele, wanda ke matsayin manajan darakta a bankin Zenith, a matsayin gwamnan CBN a 2014.
Haka nan kuma tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bayan ya karɓi mulki a 2015 ya ci gaba da aminta da tsohon ma'aikacin bankin.
Farfesa Moghalu ya ce:
"Zan faɗi ra'ayina game da abin da Emefiele ya yi a matsayin gwamnan CBN duk da wasu da ya kamata su yi faɗi hangensu sun yi shiru."
"Babu tantanma ko waswasi shi ne mafi muni wanda ya lalata komai a matsayin gwamnan CBN wanda ba a taɓa yin kamarsa ba a tarihin Najeriya."
"Bai cancanta ba kuma bai ma shirya riƙe mukamin ba kuma a iya bayanan da suka fito game da ayyukan da ya yi, babu shakka mutum ne mara gaskiya."
Jerin yan siyasar da aka ɗaure a 2023
A wani rahoton na daban kun ji cewa wasu ƴan siyasa masu faɗa a ji a Najeriya sun tsinci kansu a gidan gyaran hali saboda wasu dalilai.
Legit Hausa ta tattaro muku manyan ƴan siyasa biyu da kotu ta sa suka girbi laifukan da suka shuka a shekarar 2023 da ke dab da karewa.
Asali: Legit.ng