NDLEA Ta Kama Jika Da Kankansa Mai Shekara 70 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Kama Jika Da Kankansa Mai Shekara 70 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

  • Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta yi nasarar kama wata yar shekara 70 da jikanta kan safarar miyagun kwayoyi a Legas
  • Jami'an na NDLEA kuma sun yi nasarar kama wani kaya da aka shigo da shi Najeriya ta jirgin sama gabanin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara
  • Kayayyakin da jami'an na NDLEA suka kama sun kunshi kwayoyin tramadol da aka haramta amfani da shi a kasar da wasu daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Abuja - Jami'an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama wata mata mai shekara 70, Selifat Funke Cole da danta, Babajide Ayorinde Cole kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, a Abuja.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Jami'an NDLEA sun kama jika da kakansa yar shekara 70 a Legas
NDLEA sun kama mata yar shekara 70 da jikanta kan safarar miyagun kwayoyi. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, jami'an NDLEA a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, sun kai samame wani gida a Mushin a Legas inda aka kama matar mai shekara 7- da danta tare da kilogiram 117.900 na ganyen wiwi mai.

A jihar Edo, an kama wasu mutane biyar sanye da tufafi irinta jami'an NDLEA dauke da bindiga da pistol da aka kirkira da katako bayan samun bayanan sirri da ya nuna cewa suna shiga irinta jami'an hukumar suna kai samame ba bisa ka'ida ba.

Wadanda ake zargin sun hada da: Sebastine Asekiamhe, 22; Raymond Otaru, 28; Emmanuel Wisdom, 23; Solomon Edogamhe, 27; da Bonaventure Oghibui, 22.

Yayin da wasu daga cikinsu sanye da kayan NDLEA sun tsere, an samu kwalban magani mai dauke da sinadarin kodin tare da wadanda aka kama.

Ya kuma ce hukumar ta NDLEA ta dakile yunkurin da bata-gari da dama suka yi na shigo da miyagun kwayoyi kasar yayin bukukuwa inda jami'an suka kwace kwayoyin tramadol da nauyinsu ya mai miligiram 225, dubban kwalaben kodin da buhun ganyen wiwi da ya iso kasar gabanin kirsimeti.

Kara karanta wannan

Ba Dani Ba: Sheikh Dahiru ya yi martani kan wasikar da aka ce ya rubuta kan rikicin Abba da Gawuna

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"A filin tashin jiragen sama na Murtala Muhammed, Ikeja Legas, jami'an NDLEA tare da hadin kan sauran masu ruwa da tsaki sun dakile dukkan dabarun da masu safarar miyagun kwayoyi suka yi na shigo da tramadol guda 7,500,000 mai nauyin 225mg cikin kasar.
"An shigo da kayan a ranar Juma'a ta Turkish Airline ba tare da rubuta kasar da aka kera shi ba. Baya ga cewa wannan ne karon farko da za a kwace irin wannan abin daga jirgin, wannan ne karo na farko da ke zuwa daga Jamus," in ji Babafemi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164