Ana Tsaka da Shirin Kirsimeti, ’Yan Bindiga Sun Sheke Gomman Mutane a Jihar Filato

Ana Tsaka da Shirin Kirsimeti, ’Yan Bindiga Sun Sheke Gomman Mutane a Jihar Filato

  • An bayyana yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka hallaka mutane sama da 10 a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya
  • An ruwaito cewa, an kashe mutanen ne a lokacin da suke tsaka da barci a gidajensu, lamari mai daukar hankali
  • Gwamnan jihar ya tura sakon gaggawa ga jama'a da sauran masu ruwa da tsaki kan wannan bakin lamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Filato - Akalla mutane 16 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a kauyen Mushu da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aiki da jami’an wanzar da zaman lafiya a jihar, Captain Oya James, ya tabbatar wa Daily Trust aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Matattu ma basu tsira ba yayin da 'yan fashi suka yi wa gawa tatas a cikin mota, bayanai sun fito

An kashe jama'a a jihar Filato
'Yan ta'adda sun kashe mutane a Filato | Hoto: DefenseHQ
Asali: Twitter

A cewar Captain James, 'yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Asabar yayin da mazauna unguwar ke barci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru a Filato bayan harin

Ya kara da cewa:

“Bayan harin, an tura jami’an tsaro domin dakile duk wani dagulewar doka da oda a yankin. An tada hankali bayan faruwar lamarin amma an shawo kan lamarin.”

A halin da ake ciki, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa al'ummar, yana mai bayyana harin a matsayin dabbanci, rashin tausayi da rashin imani, Tribune Online ta tattaro.

A wata sanarwa da Daraktan yada labai da hulda da jama'a ya na Gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ya ce gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da tabbatar da sun fuskanci fushin doka.

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Yan sanda sun gano bindigu an boye su cikin buhu a wata jihar Kudu

Wane yanayi gwamnan jihar ya shiga bayan harin?

Bare ya ce gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin, inda ya bukaci al’umma a fadin jihar da su sanya ido sosai, tare da kai rahoton duk wani abin zargi ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.

Jihar Filato dai na daga jihohin Arewacin Najeriya da suka yi kaurin suna wajen farmakin 'yan ta'adda.

Ba yanzu aka fara kashe mutane a Filato ba, an sha yin hakan a lokuta daban-daban na tsawon shekaru sama da 20.

An farmaki jama'a a jihar Kwara

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton makasa ne sun kashe wani Dokta David Adefikayo, shugaban asibitin Dafikayo a gidansa da ke Kanbi a karamar hukumar Moro a jihar Kwara.

Jaridar Daily Trust ta ce maharan sun shiga gidan marigayin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Alhamis inda suka yi wa likitan kisan gilla a gaban matarsa ​​da ƴaƴansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.