Ministar Buhari Ta Shiga Uku, EFCC Ta Lalubo Satar Naira Biliyan 37 a Gwamnatin Baya
- Hukumar EFCC ta yi bincike ta gano yadda aka sulale da N37,170,855,753 daga asusun gwamnatin tarayya
- Bayanai sun nuna an karkatar da kudin ne daga ma’aikatar jin kai da bada agaji a cikin shekaru kimanin hudu
- EFCC mai yaki da rashin gaskiya za ta iya jefa Sadiya Umar-Farouk a matsala domin ita ce Minista a lokacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta gano N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar a gwamnatin tarayya.
Rahoton Punch ya ce ana zargin an tafka wannan badakala a ma’aikatar jin kai da bada agaji a karkashin Sadiya Umar-Farouk.
EFCC: 'Dan kwangila ya yi gaba da N37bn
Bayanai sun nuna an yi awon gaba da kudin daga asusun gwamnati, an tura asusu 38 na wani ‘dan kwangila a bankunan ‘yan kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan kwangilan da ake zargin an aikawa wadannan makudan kudi shi ne James Okwete.
Da kudin su ka shigo hannun James Okwete, shi kuma sai ya aika N6,746,034,000.00 zuwa ga wasu ‘yan canji, a nan ya karbe miliyoyin.
‘Dan kwangilar ya karbi N540,000,000.00 daga hannun ‘yan canjin, wanda ya yi amfani da su wajen sayen manyan motoci da gidaje.
Rahoton ya ce an kashe N288,348,600.00 a kan motoci sannan aka saye katafaren gidaje har na N2,195,115,000.00 a Abuja da Enugu.
Yadda aka yi amfani da kamfanoni
Kamfanoni 53 da ake zargin suna da alaka da Okwete aka yi amfani da su a badakalar.
Binciken da aka yi a hukumar CAC ya tabbatar da Okwete shi ne Darekta a 11 daga cikin kamfanoni 53 da ake zargi da hannu a lamarin.
A sauran kamfanonin 42, BVN sun nuna ‘dan kwangilar yana cikin wadanda su ke kula da asusun kamfanonin da ke manyan bankuna.
Lambar Sadiya Umar-Farouk ya fito
Sadiya Umar-Farouq ce ministar farko a ma’aikatar jin kai, bada agaji da cigaban al’umma da Muhammadu Buhari ya kirkiro a 2019.
Takardun binciken sun ce daga 2019 zuwa 2023, Okwete ya karbi N37,170,855,753.44 daga asusun ma’aikatar ba tare da an bin doka ba.
Damar da Sadiya Umar-Farouk ta samu
Bayan kirkiro ma’aikatar jin-kai a 2019 ne aka samu labari wasu tsare-tsaren gwamnati sun koma hannun Sadiya Umar Farouk.
Da farko Yemi Osinbajo ya fara kula da NSIP a lokacin ya na mataimakin shugaban kasa. Yanzu 'yan majalisa na kokarin canza tsarin.
Asali: Legit.ng