Abun da ya kamata ku sani game da zababbiyar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouq

Abun da ya kamata ku sani game da zababbiyar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouq

Sadiya Umar Faruq ta kasance daya daga cikin jerin mutanen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayensu majalisar dattawa, domin a tantance su a matsayin ministocinsa.

Wannan ya sa muka zakulo maku da takaitaccen tarihin rayuwarta, musamman tafiyarta a siyasar kasar.

Karatu: Sadiya ta yi karatu a kwalejin mata na tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara sannan ta halarci jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jihar Kaduna inda ta samu kwalin digiri a fannin kasuwanci a 1998.

Daga nan sai ta ci gaba da karatu don samun kwalin digiri na biyu a fannin harkokin kasashen waje da diflomassiya a 2008 sannan ta kuma yi digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 2011.

Aiki: Daga 1999 zuwa 2000, Sadiya tayi aiki tare da majalisar dokokin Najeria, karkashin kwamitin majalisar dattawa kan sufurin jirgin sama da kuma kwanitin majalisar dattawa kan kasafin kudi.

Tsakanin 2001-2003, ta kuma yi aiki a matsayin manajar gudanarwa a kamfanin Pinnacle Travels da Tour Ltd kafin ta yi aiki da hukumar majalisar dokokin tarayya a matsayin jami’ar gwamnati a 2003 inda ta kai matsayin babbar jami’at gwamnati kafin ta bari hukumar a 2010 domin tsunduma harkar siyasa.

KU KARANTA KUMA: Jerin ministoci 13 da suka samu dawowa majalisar Buhari

Siyasa: Tsakanin 2011-2013, ta zama ma’ajiyar kudi na jam’iyyar CPC na kasa, sannan daga bisani ta zama ma’ajiyar kudi na wucin gadi a jam’iyyar APC daga 2013-2014 kafin a nada ta a matsayin mamba a kwamitin kamfen din shugaban kasa, tayi aiki a sashin gudanarwa, tsare-tsaren zabe da kula a lokacin zaben 2015 wanda APC tayi nasara.

A ranar 26 ga watan Satumba, 2016, an nada Sadiya a matsayin babbar kwamishinar tarayya na hukumar kula da harkokin baki da yan gudun hijira wato NCFRMI.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel