Hotuna Sun Bayyana Yayin da Shettima, Gwamnoni Suka Halarci Daurin Auren Dan Abacha a Maiduguri

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Shettima, Gwamnoni Suka Halarci Daurin Auren Dan Abacha a Maiduguri

  • Garin Maiduguri da ke jihar Borno ya yi cikar kwari na manyan masu fada aji a Najeriya a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, gwamnoni da jiga-jigan gwamnati sun halarci daurin auren Musatapha Abacha
  • An daura auren dan tsohon shugaban kasa Sani Abacha da kyakkyawar amaryarsa Safa Tijjani Saleh Geidam a masallacin Mohammed Ali da ke garin Maiduguri

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Maiduguri, Jihar Borno - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci daurin auren dan marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha, Mustapha Sani Abacha.

An daura auren Mustapha da kyakkyawar amaryarsa Safa Tijjani Saleh Geidam, a babban masallacin Mohammed Ali da ke garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu, Zulum da wasu manyan ƙusoshi da zasu halarci gasar karatun Alqur'ani Mai Girma

Daurin auren dan Abacha
Hotuna Sun Bayyana Yayin da Shettima, Gwamnoni Suka Halarci Daurin Auren Dan Abacha a Maiduguri Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wasu gwamnoni da suka hada da na gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, takwaransa na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf duk sun samu halartan daurin auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu da shugaban kamfanin man fetur na kasa, Mele Kyari duk sun hallara a wajen daurin auren.

Sauran wadanda suka halarci daurin auren sune shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kaka Shehu Lawan, mambobin majalisun tarayya da na jiha da sauran masu fada aji.

Kakakin ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya fitar da karin hotunan daurin auren a shafinsa na X, wanda aka fi sani da ta Twitter a baya. Ga su a kasa:

Shettima ya yiwa Peter Obi tatas

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

A wani labari na daban, mun ji cewa fadar shugaban kasa ta dauki lokaci inda ta mayar da martani ga Peter Obi na LP a kan sukar da yake yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Raddin ya fito daga ofishin Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ta bakin kakakinsa, Stanley Nkwocha a Twitter a ranar Talata.

Mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasar ya zargi ‘dan takaran na 2023 da bata gwamnatin Bola Tinubu saboda haushin fadi zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng