2024: Malamin Addini Ya Yi Hasashe Mai Cike da Damuwa Game da Tinubu, Wike da Nnamdi Kanu

2024: Malamin Addini Ya Yi Hasashe Mai Cike da Damuwa Game da Tinubu, Wike da Nnamdi Kanu

  • Primate Elijah Ayodele na cocinINRI Evangelical Spiritual ya fitar da hasashensa game da 2024, wanda ke cike da damuwa
  • Malamin addinin ya saki hasashensa game da abubuwan da za su faru a shekarar 2024 mai shafuka 91
  • Wasu daga cikin manyan hasashensa sun kunshi manyan sunaye kamar na Shugaban kasa Bola Tinubu, Nyesom Wike, Nnamdi Kanu da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen abubuwan da za su faru da wasu manyan mutane kamar su Shugaban kasa Bola Tinubu, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da shugaban IPOB a 2024.

A cewar Ayodele, Allah ya nuna masa wasu abubuwa, da ke nuna cewa za a samu sabanin siyasa da zai kai ga barkewar rikici tsakanin Shugaban kasa Bola Tinubu da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Nazarin Shekarar 2023: Peter Obi, Kwankwaso da ‘Yan siyasa 6 da suka fi kowa tasiri a shekarar 2023

Fasto Ayodele ya yi hasashe game da 2024
Primate Ayodele Ya Yi Hasashe Mai Cike da Damuwa Game da Tinubu, Wike da Nnamdi Kanu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike, Primate Elijah Ayodele
Asali: Facebook

Malamin addinin ya bayyana cewa sabanin zai sa jam'iyyar APC mai mulki yin danasanin sako Wike cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Primate Ayodele ya ce:

"Ubangiji ya nuna mani cewa Shugban kasa Tinubu da Nyesom Wike za su samu sabanin siyasa da zai kai ga fada. Ubangiji ya ce daga bisani APC za ta yi danasanin kawo Wike cikin jam'iyyar. Wike yana da wani kudiri da ba zai taba cimmawa ba."

Hasashe game da Nnamdi Kanu

Malamin ya kuma yi hasashe game da masu fafutukar biyafara, inda ya hango cewa Nnamdi Kanu zai shafe tsawon lokaci a kulle.

Haka kuma, Ayodele ya yi hasashen rikici tsakanin Kanu da Simon Ekpa, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin almajiran Kanu.

Sahara Reporters ta nakalto Primate Ayodele yana cewa:

"Ubangiji ya ce SAMUEL EKPA da NNAMDI KANU za su yi fada. Na hango rabuwar kai a cikin IPOB. Ubangiji ya ce ba za a yaba ba wadanda ke fafutukar ganin an saki Nnamdi Kanu ba a 2024.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

“Idan ba su yi taka-tsan-tsan ba, Nnamdi Kanu zai fuskanci hukuncin dauri mai tsawo. Ubangiji yace bai kamata a daure Nnamdi Kanu ba. Bai cancanci alfarma na musamman ba amma dai ayi adalci."

Ya bukaci yan Najeriya da su yi addu’a don gujewa barkewar gobara, hare-hare ko rasa wani a fadar shugaban kasa, ganin yadda ya hango wani mummunan rikici da ke bukatar addu’a domin a kauce masa.

Primate Ayodele ya kuma ce:

"Allah ya bayyana mini cewa ASO VILLA na bukatar tsarkakewa saboda abubuwan ban mamaki da ke shawagi da kewayen wurin."

Fasto Adeboye ya ja hankalin yan Najeriya

A wani labarin kuma, babban faston cocin RCCG, Fasto Richard Adeboye, ya fada ma yan Najeriya abun da ya kamata su yi wa shugabannin siyasa a kasar.

Adeboye ya ce ya kamata yan Najeriya su taya shugabanni a kasar da addu'a maimakon yin zanga-zanga da tsine masu, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng