“Yadda Mutum Zai Yi Kudi Bayan Ya Isa Canada”: Matashi da ke Zaune a Turai Ya Yi Muhimmin Bayani
- Wani mutum mazaunin Canada ya bayyana hanyoyi biyu da mutum zai bi ya tara dukiya a kasar ta Arewacin Amurka
- Yayin da mutane da dama ke son tura kudi kasashensu don gina gidaje, mutumin ya shawarce su kan daina yin haka
- Ya ce maimakon haka abu na farko shine su fara tara kudi a Canada sannan ya yi bayanin yadda za su mallaki kadarori masu kawo riba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani mazaunin New Brunswick ya yi bayanin yadda baki za su iya samun makudan kudade a Canada.
A wani bidiyo mai tsawon mintuna 9 a TikTok, dan Najeriyan ya shawarci jama'a da su daina tura kudi gida don gina masu gidaje.
Yadda za ka yi kudi a Canada
Ya ce mataki na farko shine fara tara kudi don mutum ya iya siyan fili ko filaye, yana mai cewa akwai yankunan da za su iya samunsu a arha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan nan, ya ce mutum na bukatar gina kudaden shigarsa. Ya yi bayanin cewa da kudin shiga mai gwabi, mutum zai iya tukarar bankuna ko kamfanoni masu zaman kansu da ke bayar da bashin kudin gini don taimakawa mutum wajen gina filin da ya mallaka.
"Yana iya kasance gidan da kake mafarko ko kuma gida da za kake son bayar da haya," cewar shi.
Dan Najeriyan ya ci gaba da cewa ana tantance gidan da aka gina bayan shekara guda domin a tabbatar da darajarsa. Lokacin da aka tabbatar da ya kara daraja, ya ce mutum zai iya tunkarar banki don samun kudin da ya yi daidai da gidan da ya kara daraja.
Ya kara da cewar za a iya zuba kudin da aka samu daga banki a wani kadarar. A cewarsa, kudin da ake bayar da rance yana da sauki sosai kuma harajin wanda ya mallaki gida a karo na farko na da sauki.
Wata hanyar samun arziki a Canada
Mutumin ya ce wata hanyar samun arziki a Canada ita ce ta hanyar siyan gidajen da aka yi watsi da su. Ya ce ana sayar da gidajen da aka yi watsi da su a kan farashi mai rahusa.
Idan mutum ya sami irin wadannan gidaje, ya ce sai a gyara su sannan dilalli zai yi kudin sabon da darajarsa ya karu.
Da zarar an yi haka, ya ce mutum zai iya sake zuwa banki don samun kwatankwacin kudin da ya yi daidai da darajarsa.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
halabitimoty ta ce:
"A kullun ina kaunar bidiyonka, yana da bayanai masu amfani."
lemmefamous ya ce:
"Allah ya albarkaceka da dukkan bayanan da ka bamu."
oluwaseunakanbi84 ya ce:
"Muna godiya da shawararka mai cike da gaskiya mutane irinka ne muke so su wayar mana da kai."
Matashi ya tashi kan mutanen kauye
A wani labarin kuma, mun ji cewa a wani bidiyo da ya yadu, wani mutumi ya haddasa cece-kuce bayan ya isa kauyensa a wata mota mai budaddiyar sama.
Yara da manya sun kewaye shi yayin da suke kallo cike da mamaki lokacin da mutumin ke yi kamar bai san yana daukar hankali ba.
Asali: Legit.ng